Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya taya musulman Najeriya murnar shiga watan Ramadan

Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya taya musulman Najeriya murnar shiga watan Ramadan

- Yemi Osinbajo ya roki Musulmai da suyi amfani da lokacin Ramadan gurin tunawa da kalubalen da kasa ke fuskanta

- Mukaddashin shugaban kasar ya yi kira ga Musulmai da su roki tarin falala daga watan Ramadan

- Osinbajo ya yi kira gay an Najeriya da su ci gaba da yima shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya roki yan Najeriya musamman Musulmai da suyi amfani da watan Ramadan gurin tunawa da kalubalen da kasar ke fuskanta sannan kuma hada hannu da gwamnatin Buhari domin shawo kan kalubalen.

Ya bada shawaran a sakon sa domin taya musulmai murna a Najeriya kamar yadda suka shiga watan Ramadan, wata mai tsarki na azumi da ibadah.

Mukaddashin shugaban kasar ya roki Musulmai da su nemi tarin falala daga watan Ramadan ta hanyar koyi da koyarwan annabi Muhammadu a dukkan ayyukansu, na gida da waje.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Hukumar NSCIA ta sanar da fara azumin watan ramada a Najeriya

Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya taya musulman Najeriya murnar shiga watan Ramadan

Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ya taya musulman Najeriya murnar shiga watan Ramadan

Ya bukaci Musulmai da suyi amfani da watan Ramadan gurin sabonda soyayya da zaman lafiya da annabi Muhammadu ya koyar, sannan kuma suyi aiki don cimma su.

Ya bayyana cewa wannan watan ne na ibadah da kuma naiman kusanci ga Allah madaukakin sarki.

Mukaddashin shugaban kasar ya yi kira ga yan Najeriya da suyi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da kasa baki daya addu’a.

A yayinda Osinbajo ya ke taya Musulmai murnan watan Ramadan, ya bukaci da su tuna gajiyayyu a kasar a irin wannan lokaci na musamman.

KU KARANTA KUMA: Kakaki Yakubu Dogara ya kai karan gwamnan jihar Bauchi wajen Sarkin Musulmi

Bisa ga rahoton da NAIJ.com ta kawo a baya, Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya kaddamar da ranar Asabar, 27 ga watan Mayu a matsayin 1 ga watan Ramadan, 1438 AH, inda ya umurci musulmai da su fara azumi.

Abubakar ya sanar da ganin sabon wata a Sokoto a ranar Juma’a, a wata sanarwa.

Sultan ya bayyana cewa an ga wata a jihohi da dama a kasar wanda suka hada da Kebbi, Lagas, Adamawa, Bauchi, Delta, Cross River da kuma Benue.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku na wani Kirista da ya karbi musulunci:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel