Kakaki Yakubu Dogara ya kai karan gwamnan jihar Bauchi wajen Sarkin Musulmi

Kakaki Yakubu Dogara ya kai karan gwamnan jihar Bauchi wajen Sarkin Musulmi

Rikicin siyasan da ke faruwa a jihar Bauchi ta canza zani yayinda kakakin majalisan wakilai Yakubu Dogara yayi kira ga Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, ya sa baki cikin rikicin da gwamnan jihar keyi da shi.

Dogara a wata wasika ya kai karan gwamna Abubakar cewa yana tayar da kura kan gyaran wasu masallata a Bogoro, Dass, da Tafawa Balewa.

Haka zalika ya tura wannan sako ga sarkin Bauchi, HRH Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Baba Lau da Sheikh Sanni Yahya Jinjir.

Kakaki Yakubu Dogara ya kai karan gwamnan jihar Bauchi wajen Sarkin Musulmi

Kakaki Yakubu Dogara ya kai karan gwamnan jihar Bauchi wajen Sarkin Musulmi

Dogara yayi bayani a cikin wannan wasikar cewa ya fara gyaran wasu masallatai a mazabarsa amma gwamnan jihar ya umurci sarakunan garin su hana ayyukan.

Ya siffanta wannan a matsayin kama karya, duk da cewa mutanen garuruwan na sa ran karashe ayyukan gyare-gyaren.

KU KARANTA: Wike yayi barazanar barin jam'iyar PDP idan Sheriff yayi nasara a kotu

Dogara yace wannan abun kunya ne da gwamnan ya nace cewa kada wanda ya sake ya bari kakakin ya gudanar da wani aikin gyara domin yabo.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel