Wike yayi barazanar barin PDP idan Sherrif ya samu nasara a kotun koli

Wike yayi barazanar barin PDP idan Sherrif ya samu nasara a kotun koli

A yau Juma’a ne gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yayi alwashin cewa ba zai taba iya aiki karkashin jagorancin shugaban jami’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Ali Modu Sheriff idan ya samu nasara a kotun koli.

Yayinda yake hira a gidan talabjin na Channels, gwamnan jihar Ribas din ya jaddada cewa aiki karkashin Sheriff ta sabawa al’adanshi.

Wike ya kara da cewa zai fita daga jam’iyyar idan kotun kolin ta baiwa sheriff nasara.

Rikicin PDP: Wike yayi barazanar barin PDP idan Sherrif ya samu nasara a kotun koli

Rikicin PDP: Wike yayi barazanar barin PDP idan Sherrif ya samu nasara a kotun koli

Yace : “Dalilin da yasa muke bibitan wannan abu shine sanin matsayar doka kuma ayi abu yadda ya kamata.

“Da wuyan tsiya ni inyi kasance karkashin Sheriff idan kotun koli ta bashi nasara. Ba zan iya cewa zan bar jam’iyyar ba amma zanyi zabi na.”

KU KARANTA: Tattalin arzikin Najeriya ya girgizza

“Shin ka ga mutanen da ke zagaye da Sheriff ne? Shin jam’iyyar na da mahanga da irin wannan mutum? Kuma kana son in koma inyi aiki karkashin irin wannan mutum? Wannan ya sabawa addini na da kuma al’ada ta, ba zan iya haka ba.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel