Hukumar yan sanda zata sake daukan ma’aikata 35,000 – Shugaban kwamitin yan sanda a majalisa

Hukumar yan sanda zata sake daukan ma’aikata 35,000 – Shugaban kwamitin yan sanda a majalisa

Shugaban kwamitin yan sanda na majalisar wakilan tarayya, Alhaji Haliru Jika, yace hukumar yan sandan Najeriya zata dauki sabbin ma’aikata 35,000 ba da dadewa ba.

Alhaji Haliru Jika, mai wakiltar mazabar Ganjuwa/Darazo a jihar Bauchi ya bayyana hakan ne yayinda yake tattaunawa da manema labarai a Bauchi yau Juma’a.

“Yanzu muka gama daukan hafsoshi 10,000 kuma ba da dadewa ba zamu dauki guda 35,000.

“Wanda kuma fara yi mun dauki hafsoshi 1500, kanikawa, likitoci da sauransu kuma 1,000. Kana kuma mun dauki sauran 7,500 a matsayin yan sandan aiki.”

“Yanzu kuma zamu dauki 35,000 ba da dadewa, zamuyi shi sosai saboda babu isassun yan sanda a kasa.

Hukumar yan sanda zata sake daukan ma’aikata 35,000 – Shugaban kwamitin yan sanda a majalisa

Hukumar yan sanda zata sake daukan ma’aikata 35,000 – Shugaban kwamitin yan sanda a majalisa

“Aikinmu na majalisa ne shine karfafa tsaron Najeriya , shi yasa mukayi tunanin yanada muhimmanci mu kara jami’an yan sanda domin karfafar tsaron kasa.”

KU KARANTA: Dalar Amurka, kalli abinda ya zama

“Shi yasa mukayi niyyan daukan 10,000 da farko lokacin da shugaba Muhamadu Buhari za hau mulki kuma ya bada umurnin daukan jami’ai 10,000.

“Kuma yanzu ya sake bada wani umurni a dauki sauran 35,000.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel