Dan shekara 18 ya yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade a Katsina

Dan shekara 18 ya yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade a Katsina

- An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a kotu a bisa aikata laifin fyade

- An rahoto cewa yayi ma kanwar sa mai shekaru 8 a duniya fyade

An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a kotu a bisa aikata laifin yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne a rukunin gidaje na ‘Steel Rolling Mills’ da ke kan titin Dutsinma a jahar Katsina

KU KARANTA KUMA: Babu ranar gyara wuta a Najeriya Inji Majalisar Dattawa

Alkalin Kotun, mai shari’a Hajiya Falile Dikko ta bayar da umarnin a tsare matashin a gidan maza har zuwa ranar 29 ga watan Yuni yayin da za a saurari karar.

‘Yan sanda sun bayyana wa kotun yadda matashin ya yaudari kanwar ta shi zuwa cikin bandaki, inda ya aikata aika aikar akan ta da karfin tuwa.

Laifin ya saba da sashe na 390 na kundin dokar ‘Penal Code’.

Tuni aka kai yarinyar asibiti inda aka duba lafiyar ta tare da yi mata magani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel