Gwamna Ganduje zai kashe naira miliyan 300 akan ciyarwar Azumi

Gwamna Ganduje zai kashe naira miliyan 300 akan ciyarwar Azumi

- Gwamnatin jihar Kaduna ta samu cikas daga hannun kotu dangane da kasuwar barci

- Kotun ta hana Gwamnatin rusa kasuwar barci har sai ta kammala sauraron kara

Gwamnatin jihar Kano ta ware naira miliyan 300 don ciyarwa kyauta a azumin bana da ake sa ran faraway aranar Asabar 27 ga watan Mayu.

Shugaban kwamitin ciyarwar Malam Ibrahim Kankarofi ne ya bayyana haka a yayin taron shuwagabannin kwamitin ciyarwar na dukkanin kananan hukumomin jihar, 44 daya gudana a gidan gwamnati.

KU KARANTA: Yadda wani mutum ya guntule ma direban mota hannu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar yana fadin gwamnati zata yi iya bakin kokarinta don tabbatar da ganin an samu nasara a yayin aikin, sa’annan yace duk wanda aka kama da karkatar da kayan abinci za’a hukunta shi.

Gwamna Ganduje zai kashe naira miliyan 300 akan ciyarwar Azumi

Ciyarwar Azumi

A cewar Kankarofi, a shirin ciyarwar azumin bana, an za’a kara nau’o’in abinci kamar su taliyar Spaghetti da Macaroni da ire irensu, sa’annan yace gwamnati ta shirya ciyarwar ne domin taimaka ma talakawa.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito jagoran tawagar shuwagabannin kwamitin ciyarwar na kananan hukumomi 44, Abba Shehu yayi alkawarin zasu gudanar da aikinsu yadda ya kamata da rikon amana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Osinbanjo yayi zance:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel