Yanzu yanzu: Kotu ta hana El-Rufai rusa kasuwar barci

Yanzu yanzu: Kotu ta hana El-Rufai rusa kasuwar barci

- Babban kotun jihar Kaduna ta dakatar da gwamna El-Rufai daga rusa kasuwar barci

- Shuwagabannin yan kasuwar barci ne suka shigar da gwamnati kara

Babban kotun jihar Kaduna ta dakatar da gwamnatin jihar Kaduna daga rusa fitacciyar kasuwar nan dake cikin garin Kaduna, kasuwar barci, har sai ta kammala sauraron karar da yan kasuwar barci suka shigar.

Alkalin kotun mai shari’a Mohammed Bello ya umarci dukkanin bangarorin dasu saurara ga daukan kowanne irin mataki har sai kotu t agama sauraren karar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Hukumar Soji ta ƙaddamar da sabon sansanin dakarun sojojin ƙasa a Kafanchan

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wasu mutane goma sha shidda ne suka shigar da gwamnatin jihar Kaduna da hukumar kasuwannin jihar ta Kaduna kara a madadin yan kasuwan barci don a hana su rusa kasuwar.

Yanzu yanzu: Kotu ta hana El-Rufai rusa kasuwar barci

Kasuwa

Wadanda suka kai karar sun hada da Auwalu Hussain, Kabiru Usman, Aminu Ahmed, Bawa Ahmed, Josia Sunday, Ndubueze Egbo-Ogu, Augustine Sunday, Ali Abdulhamid, Maryam Abubakar, Rabiatu Musa, Latifah Yusuf, Amina Abdulrauf, Aishatu Ibrahim, Hafsat Uba, Sa’adiya Ahmed da Wasilat Ahmed.

Lauyan masu kara Mista Elisha Kurah, SAN ya bukaci kotu data dakatar da rushe kasuwar, sa’annan ya roki kotu data bayyana idan gwamnati nada ikon rushe kasuwar . sa’annan lauyan ya danganta bukatarsa ga sashi na 7(1) da (5) na kundin tsarin mulkin kasa.

Lauya Kura ya nemi kotu ta tabbatar da idan gwamnan jihar nada daman sallamar yan kasuwan ko a’a, daga karshe lauyan ya bukaci kotu ta hana gwamnan jihar rusa kasuwar, sa’annan kuma kotu ta yanke hukuncin cewa gwamnatin jihar bata da ikon kwace kasuwar daga hannun karamar hukuma zuwa ga yan kasuwa.

Bugu da kari, lauyan ya bukaci kotu ta yanke hukuncin cewa gwamnatin karamar hukuma ke da daman kula da kasuwannin jihar, musamman jihar Kaduna, don haka lauyan ya kara neman wata bukata daga kotu data bayyana barazanar rushe kasuwar da gwamnatin jihar tayi ma kasuwan a matsayin karan tsaye.

Daga karshe alkali Mohammed Bello ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin kudancin Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel