Aiki sai mai shi: Boka ya damfari wani mazaunin ƙasar Amurka naira miliyan 4

Aiki sai mai shi: Boka ya damfari wani mazaunin ƙasar Amurka naira miliyan 4

Jaridar Daily Post ta ruwaito jami’an yansanda na musamman dake jihar Legas sun yi caraf da wani boka mai shekaru 42, Abidoun David kan zarginsa da damfarar wani dan Najeriya, Kazeem mazaunin kasar Amurka.

Boka David ya zambaci Kazeem ne zambar kudi, wuri na gugan wuri har naira miliyan hudu da sunan zai yi masa tsafin samun arziki.

KU KARANTA: An kama ɗalibai 32, 8 sun jikkata sakamakon rikicin zaɓe a kwalejin Ilimi

A shekarar 2015 ne Kazeem, wanda ya kasance direban tasi ne a kasar Amurka ya hadu da boka David bayan an tura masa katin waya bisa kuskure, daga layin bokan, shine sai Kazeem ya mayar masa da katin nasa.

Aiki sai mai shi: Boka ya damfari wani mazaunin ƙasar Amurka naira miliyan 4

Boka Abiodun

Wannan karamci da Kazeem yayi ma boka David ya sanya bokan jin dadi tare da bayyana masa cewar zai saka masa ta hanyar yi masa tsafin samun arziki.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wani makusancin Kazeem yaan fadin “Bokan ya kai Kazeem har wani dakin tsafe tsafe a jihar Ogun, inda yayi masa siddabaru, takardu suka koma kudi, daga nan ne Kazeem ya yarda da shi

“Ya turo ma Kazeem wasu hade hade day ace zasu mayar da Kazeem gwarzo, sai bayan dawowansa Amurka ne sai boka ya fara addaban Kazeem daya bashi kudi, baya da wanda ya bashi a Najeriya. Shi kuwa Kazeem yace ba zai bayar ba, tun da dai tsafin bai yi aiki ba.

“Daga nan ne Bokan yayi baraznar sauya hade haden daya baiwa Kazeem su koma guba, da zasu kashe shi, daga nan fa sai Kazeem ya tsorata ya cigaba da biyan boka kudi, kuma ya gargade shi da kada ya kuskura ya fada ma kowa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel