Yadda wani mutum ya guntule ma direban mota hannu

Yadda wani mutum ya guntule ma direban mota hannu

- Wani mutum ya gurfana gaban kotu sakamakon zargin guntule ma wani hannu

- Kotu ta bada belinsa akan naira dubu hamsin

An gurfanar da wani matashi dan shekaru 25, Yekini Balogun a gaban kotu a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu kan tuhumarsa da ake yi da aikata ma direban babbar mota danyen aiki, inda ya cizge masa hannu.

Dansanda mai kara Inspekta Ezekiel Ayorinde yace wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Maris a unguwar Afariogun na jihar Legas, dansandan yace akwai sauran abokan aikin Balogun da suka arce, kuma a yanzu haka ake neman su ruwa a jallo.

KU KARANTA: Na shiga ban ɗauka ba: An kama ɗaruruwan baƙin haure a jihar Edo

“Wanda ake zargin ya cire ma Ibrahim Adebayo hannu da gatari ne bayan shi da abokansa sun dirar ma direba Ibrahim a wajen aikinsa, inda suka bukaci ya basu kudi, amma ya fada musu ba shi da kudi, fadin haka ya sa suka sare shi.

Yadda wani mutum ya guntule ma direban mota hannu

Kotun

“Anyi kokarin garzayawa da mutumin asibiti da gaggawa sakamakon jini da yayi ta fitarwa, yayin da suka sare shi, sun dauke masa wayar hannu, da kudinta ya kai N28,000.” Inji dansandan.

Dansandan yace laifin da ake tuhumar wanda ake zargi yaci karo ga sashi na 169, 246 da 411 na kundin hukunta miyagun laifuka na jihar Legas na shekarar 2015.

Majiyar NAIJ.com, kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito sashi na 246 na kundin ya tanadi hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari ga irin wannan laifi. Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin, kuma an bada belinsa akan kudi N50,000 da kuma wanda zai tsaya masa.

Daga nan sai alkalin kotun, ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga Yuni don cigaba da saurare.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Osinbajo yayi magana:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel