Hukumar Soji ta ƙaddamar da sabon sansanin dakarun sojojin ƙasa a Kafanchan

Hukumar Soji ta ƙaddamar da sabon sansanin dakarun sojojin ƙasa a Kafanchan

- Babban hafsan sojin kasa, Buratai ya kaddamar da sansanin Soji a Kafanchan

- An kaddamar da sansanin ne da nufin magance rikice rikicen daya addabi yankin

Rundunar mayakan sojan kasa tayi bikin kaddamar da wani sansanin sojoji a garin Kafanchan a kokarinta na magance fadace fadace daya addabi yankin kudancin Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwamandan runduna ta daya, Manjo janar Adeniyi Oyebade yace manufar samar da sansanin sojin shine domin tabbatar da zaman lafiya a garin Kafanchan da sauran yankunan kudancin Kaduna.

KU KARANTA: Na shiga ban ɗauka ba: An kama ɗaruruwan baƙin haure a jihar Edo

A jawabinsa, babban hafsan sojan kasa, laftanar janar T.Y Buratai wanda ya smau wakilcin Manjo janar R.O Yusuf yace an sansanin sojin zai zamo wajen tsare kai samame da sintiri da dakarun soji zasu dinga gudanarwa.

Hukumar Soji ta ƙaddamar da sabon sansanin dakarun sojojin ƙasa a Kafanchan

Yayin ƙaddamar da sabon sansanin dakarun sojojin ƙasa a Kafanchan

“Mun samar da sansanin nan ne da niyyar daurawa kan nasarar da aka samo dangane da yaki da satar shanu, ta’addanci da fadace fadacen addini dana kabilanci da kuma sauran miyagun ayyuka a wannan yankin.” Inji shi.

Buratai ya kara da cewa, rundunar soji dake aiki a yankin Arewa maso gabas sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi da yan ta’addan Boko Haram, sa’annan ya bayyana matsayin sabon sansanin a matsayin wani matakin farko, inda yayi alkawarin za’a sake bude wasu sansanonin a yankin.

Buratai ya kara jinjina ma injiniyoyin sojoji da suka gina sansanin, sa’annan ya jaddada goyon bayan rundunar sojin ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da mukaddashin shugaban kasa FarfesanYemi Osinbajo musamman don yadda suke baiwa rundunar goyon baya.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai daya samu wakilcin kwamandan rundunar Operation Yaki, kuma mashawarcinsa akan fannin tsaro, Kanal Yusuf Soja mai murabus, ya gode ma rundunar soji da wannan gagarumin kokari da suka yi.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito cewar: “Na gode muku babban hafsan sojojin kasa na kasa kan wannan muhimmin aiki da yayi a dan kankanin lokaci, wanda ya kwashe watanni uku kacal.” Inji Gwmanan.

Taron kaddamarwar ya samu halartan manyan baki da suka hada da Sarakunan gargajiya, da shuwagabannin kananan hukumomin yankin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli barnar da aka yi a rikicin kudancin Kaduna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel