Najeriya zata kulle ofisoshin jakadancin ta a kasashe 5

Najeriya zata kulle ofisoshin jakadancin ta a kasashe 5

- Najeriya na shirin kulle ofisoshin ta na jakadanci dake wasu kasashe

- Ministan harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka, inda yace tuni sun fara shirye shirye

Gwamnatin tarayya ta sanar da kulle wasu ofisoshin jakadancin ta a wasu kasashe guda 5, kamar yadda ministan kula da harkokin kasashen waje, Geofrey Onyeama ya bayyana.

Minista Onyeama ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu a garin Abuja, inda yace tuni an fara shirye shiryen kulle ofisoshin jakadancin Najeriya dake wasu kasashe guda 5, sai dai bai bayyana sunayen kasashen ba.

KU KARANTA: Za’a fara neman watan Ramadan ranar Juma’a – Inji Sultan

“Bama so mu bayyana sunayen kasashen yanzu, saboda a yanzu muna harhada bayanai ne, da kuma duba yadda lamarin zai shafi alakar mu da sauran kasashe, da zarar shugaban kasa ya kammala yin wannan nazari, daga nan zamu tabbatar da wadanda zamu rufe da wadanda ba zamu rufe ba.” Inji Onyeama.

Najeriya zata kulle ofisoshin jakadancin ta a kasashe 5

Minista Onyeama

Ministan yace kulle ofisoshin kansa ba karamin kudi zai ci ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaru,NAN, ta ruwaito. Tun a watan Afrilu ne minista ya shaida ma majiyar NAIJ.com cewa lallai Najeriya zata rufe wasu ofisoshin jakadancin ta dake wasu kasashe.

Minista ya danganta kulle ofisoshin da manufar gwmanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na rage kudaden da gwamnati ke kashewa ba gaira babu dalili. A yanzu haka Najeriya nada ofisoshin jakadanci guda 119 Duniya gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Satan amsa a jarabawa? laifin waye?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel