Abun tausayi: Dan wasan Kwara United Azeez Saka ya mutu

Abun tausayi: Dan wasan Kwara United Azeez Saka ya mutu

- Kungiyar kwallon kafa ta Kwara United ta rasa daya daga cikin yan wasan ta Azeez Saka a ranar Juma’a, 26 Mayu, 2017

- Saka ya fadi ya mutu ne a yayin da suke gwaji a filin kwallon jihar Kwara, Ilorin

- An kai gawarsa a dakin ajiye gawa sannan kuma ana saka ran binne shi kamar yadda addinin musulunci ta tanadar

Sanannen kungiyar kwallon kafan nan ta Kwara United ta shiga alhini a yau Juma’a, 26 ga watan Mayu sakamakon wani abun bakin ciki da ya risketa na mutuwar jarumin ta Azeez Saka.

Sharumin Ya fadi ne a lokacin da suke gwaji a safiyar ranar Juma’a a filin kwallon kafa ta jihar Kwara sannan kuma ya mutu a yayinda ake kokarin ceto rayuwar sa.

Abubakar Sylas Yusuf wanda ya kasance abokin wasan marigayin ne ya tabbatar wa NAIJ.com cewa Azeez Saka bai nuna wani alamu na rashin lafiya ba a lokacin da suke gudanar da horon a ranar Juma’a, 26 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya tayi rashin adalci ga jihohi, inji El-Rufai

Abun tausayi: Dan wasan Kwara United Azeez Saka ya mutu

Dan wasan Kwara United Azeez Saka ya mutu

“Kwarai, ina bayan sa a lokacin da ya fadi a kasa kuma a tunaninmu hutawa yake son yi, amma abun bakin ciki ya mutu bayan haka,” Sylas ya yi bayani.

Kalli wannan bidiyo na Super Eagles da NAIJ.com ta kawo maku.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel