Gwamnatin Tarayya tayi rashin adalci ga jihohi, inji El-Rufai

Gwamnatin Tarayya tayi rashin adalci ga jihohi, inji El-Rufai

- Anyi kason kudi ba jihohin adawa a zamanin PDP, an ware jihohi masu adawa da gwamnatin tarayya

- Biliyoyin kudi jihohin da ke biyayya ga jam'iyyar PDP suka samu daga Tarayya

- A shekarar 2013 an yi kason kudin kyautata muhalli aka hana jihohi 19

A taron majalisar kasa na jiya alhamis, 25 ga watan Mayu, an fidda sabon jaddawalin kason kudin kyautata muhalli, wanda ake kira ecological funds, wanda dole ne a raba wa jihohi su, domin ko-ta-kwana, da kuma aikin kula da tsarin muhalli.

Gwamna El-Rufai na Kaduna, yace za kuma a duba baya, aga yadda a da tsohuwar gwamnatin PDP tayi kason kudin ga gwamnoni da ke jibantar jam'iyyar PDP, amma aka hana na adawa.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai zamo shugaban kasar Najeriya na shekaru masu yawa

Gwamnatin Tarayya tayi rashin adalci ga jihohi, inji El-Rufai

Gwamnatin Tarayya tayi rashin adalci ga jihohi, inji El-Rufai

A lokacin tsohon shugaba Goodluck Jonathan dai, a shekarar 2013, an rabawa jihohi na PDP, APGA da LP, biliyan bi-biyu amma aka hana jihohi na jam'iyyu irinsu ACN, ANPP da CPC, duk dai domin a kassara su.

KU KARANTA KUMA: EFCC: Magu yayi alkawari cewa nan da watanni 12 za a ga abin mamaki

Malam Nasir El-Rufai dai ya ce za'ayi waiwaye adon tafiya, domin a biya kowacce jiha hakkokin da take bin tarayya, domin adalci. Jihohi irinsu Kano, Jigawa, Kwara, da Legas da Sakkwato zasu dara in dai aka biya su naira biliyan biyu-biyunsu suma. Jihohi 19 ne dai aka hana kudaden a wancan lokacin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

EFCC tayi tattakin yaki da ha'inci kwanaki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel