Babu wani cigaban da aka samu a mulkin shekaru 2 na APC - Jam’iyyar PDP

Babu wani cigaban da aka samu a mulkin shekaru 2 na APC - Jam’iyyar PDP

- Jam’iyyar adawar PDP ta jihar Neja ta caccaki gwamnatin APC cewa babu wani cigaba da aka samu a bangaren gudanar da ayyukan raya kasa a jihar bayan da gwamnatin APC ta cika shekaru biyu da hawa kan mulki a Nijeriya.

- Barrista Tanko Beji, Shugaban jam’iyyar PDP ta jihar Neja, yace gwamnonin wasu jihohi dai suna gayyato mutane domin a kaddamar da ayyuka amma a jihar Neja babu wani aiki da aka yi balle kuma a kaddamar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wasu mutanen karkara sun bayyana ra’ayoyinsu kan cikar gwamnatin APC shekaru biyu kan mulki inda wani Alhaji Abdurra’uf, dake zaune a karamar hukumar Agwara, yace sun ji dadin ziyarar da mai girma gwamna ya kai musu, da kuma gyara musu hanya da yayi.

Babu wani cigaban da aka samu a mulkin shekaru 2 na APC - Jam’iyyar PDP

Babu wani cigaban da aka samu a mulkin shekaru 2 na APC - Jam’iyyar PDP

Abdurrahman Mohammad wani direban Agwara, cewa yayi a baya sun sha fama da matsaloli na Asibiti wadanda ke ci musu tuwo a kwarya, amma gwamnati ta yi kokarin shawo kan matsalar, sai dai kuma har yanzu suna bukatar a sake duba lamarin.

Injiniya Mohammad Imam, shugaban jam’iyyar APC mai mulki a jihar Neja, yace gwamnatin APC ta samu ayyuka da ba a kammala su ba wanda yanzu haka baki daya an kammala su, domin cigaban jihar baki ‘daya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel