Kwana 1 kafin azumi: Hukumar kwastam ta kara jaddada haramcin shigowa da shinkafa daga waje

Kwana 1 kafin azumi: Hukumar kwastam ta kara jaddada haramcin shigowa da shinkafa daga waje

- Hukumar kwastam na kasa ta nanata hana shigo da shinkafa ta hanyar mota kamar yadda ta ke yaki da sumoga na kayayyaki da ba a yadda da a shigo da shi ba.

- Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam, mataimakin kwanturola Joseph Attah, ya bayyana hakan ne a wani hira da aka yi da shi na musamman inda ya ke cewa hukumar kwastam na kasa ta jijina wa manoma game da irin kokarin da su kai wajena ganin sun samar da isasshen shinkafa a kasar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce hukumar za ta ci gaba da hana shigar da shinkafa daga wasu kasashen ta hanyar mota kasar saboda a bunkasa da shinkafa a gida ta hanyar noma ta.

Attah ya ce kwanturola Janara na kwastam, kanar Hameed Ibrahim Ali ya bayyana cewa idan har za a ci gaba da samun nasaran noman shinkafa a kasan nan gaba, hukumar za ta dakatar da shigo da shinkafa daga wasu kasashen.

Kwana 1 kafin azumi: Hukumar kwastam ta kara jaddada haramcin shigowa da shinkafa daga waje

Kwana 1 kafin azumi: Hukumar kwastam ta kara jaddada haramcin shigowa da shinkafa daga waje

Ya ce, “Hukumar kwastam ta nanata hana shigowa da shinkafa ta hanyoyin iyakar kasa. Kamar yadda samar da shinkafar gida ke bunkasa a kasa. Babu shakka hukumar za ta iya bayar da shawarar hana shigo da shinkafan kwata-kwata daga kasar.”

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel