Majalisar dattijai ta bayyana goyon bayan ta ga cire iyakar shekaru wajen takara

Majalisar dattijai ta bayyana goyon bayan ta ga cire iyakar shekaru wajen takara

- Majalisar dattijan Najeriya ta bakin mataimakin shugaban majalisar Sanata Ike Ekweremadu ya bayyana goyon bayan sa ga kudurin cire shingen shekaru a wajen takara.

- Mataimakin shugaban majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wasu matasa a karkashin jagorancin wata kungiya mai suna YIAGA a ofishin sa dake a majalisar a Abuja.

NAIJ.com ta samu labarin tun farko shugabar tawagar Miss Cynthia Mbamalu ta nemi goyon bayan majalisar domin tabbatar da kafuwar wannan kudurin wanda Sanata Abdul-Aziz Nyako ya gabatar.

A wani labarin kuma, Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, ya bada tabbacin cewa majalisa ta zange damtse wajen tabbatar da dokar da zai hana yan shekarun kasa takaran zabe a kasa.

Majalisar dattijai ta bayyana goyon bayan ta ga cire iyakar shekaru wajen takara

Majalisar dattijai ta bayyana goyon bayan ta ga cire iyakar shekaru wajen takara

Yayinda yake magana da majalisar matasa ranan Laraba a Auja, Dogara yace zasuyi hakane saboda baiwa matas daman musharaka a siyasa da shugabancin kasa.

“Saboda hakan ne muka tabbatar da cewa aikinmu na kan gaba shine samar da daidaito da baiwa mata, matasa, da masu rauni dama a al’umma.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel