An gudanar da taron hada kan mabiya mabanbantan addinai da kabilu a Kaduna

An gudanar da taron hada kan mabiya mabanbantan addinai da kabilu a Kaduna

- Kungiyar ta Global Peace Foundation ta gudanar da wani babban taron domin hada kan al’umman yankin

- Kungiyar ta ce idan an daina nuna banbancin addini da na kabila a tsakanin mutane za a iya samu cikakkiyar zaman lafiya

- Mahalartar taron sun nuna jin dadinsu da godiyarsu ga muhimmancin taro

Kungiyar rajin wanzar da zaman lafiya tsakanin al’umma Global Peace Foundation, ta ce ta gano banbance-banbancen da ake yawan samu cikin al’umma ake amfani da shi wajen hada rigingimu ga tsakanin mutane.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kungiyar ta hada wani taro a yankin Afaka da ke garin Kaduna, inda aka tattara mabanbantan addinai da kabilu don jawo hankalin al’umma su fahimci banbance-banbancen da ke tsakaninsu don su zauna lafiya da juna.

Daya daga cikin shugabannin kuniygar GPF, Rev Joseph Hayaf, ya ce idan an daina nuna banbancin addini da na kabila a tsakanin mutane za a samu cikakkiyar zaman lafiya da samun ci gaba.

An gudanar da taron hada kan mabiya mabanbantan addinai da kabilu a Kaduna

Rikicin kudancin jihar Kaduna

KU KARANTA: Ana samun raguwar cutan kanjamau a Kaduna

Shima Sheikh Halliru Maraya, dake zama shugaba a kungiyar GPF, ya ce sun lakanci bayan addini al’ada na matukar taimakawa wajen samun fahimtar juna, inda yace babu yadda za a sauna lafiya ba tare da an fahimci asali ba.

Da yawa daga cikin halartar taron sun nuna jin dadinsu da godiyarsu ga muhimmancin wannan taro, wanda ya hada Musulmai da Kristoci da kuma kabilu kala daban-daban, domin samar da hadin kai da tabbatar da zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon rikicin kudancin jihar Kaduna shafi na biyu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel