Buhari zai zamo shugaban kasar Najeriya na shekaru masu yawa

Buhari zai zamo shugaban kasar Najeriya na shekaru masu yawa

- Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ya kaffa hujjar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kasance shugaban kasar Najeriya na shekaru da dama

- Gwamna Ajimobi ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu a gurin kaddamar da ofishin hukumar dake yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) shiyar Ibadan

Gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi ya kaffa hujjar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kasance shugaban kasar Najeriya na shekaru da dama.

Gwamna Ajimobi ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu a gurin kaddamar da ofishin hukumar dake yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) shiyar Ibadan.

“Munyi dace sosai d muka samu mutun mai adalci da gaskiya kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Babu ranar gyara wuta a Najeriya Inji Majalisar Dattawa

Buhari zai zamo shugaban kasar Najeriya na shekaru masu yawa

Buhari zai zamo shugaban kasar Najeriya na shekaru masu yawa cewar Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi

“Buhari ne mutumin da Najeriya ke bukata a yanzu. Mun gode ma Allah da cewan yana nan kuma zai kasance a nantsawon shekaru da dama." Cewar sa.

NAIJ.com ta tattaro inda Gwamnan ya bukaci yan Najeriya da su hada hannu da hukumar EFCC gurin yaki da cin hanci da rashawa a kasar, ya kara da cewa har yanzu ya kasance kalubale ga nasara da ci gaban kasar.

“A koda yashe shugaban kasar na gargadin yan Najeriya da cewan idan bamu kashe cin hanci da rashawa ba toh zata kashe mu, don haka, muyi hakuri mu goya ma gwamnati baya gurin yaki da rashawa.” Cewar sa.

Gwamnan ya yaba ma mukaddashin shugaban hukumar, Ibrahim Magu, cewa hukumar ta yaki da rashawa tayi gagarumin nasara.

Ajimobi ya yi kira ga majalisar dokoki, musamman majalisar dattawa da ta tabbatar da Magu domin ci gaba da samun nasara.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kun koyi bayan shugaban kasa Buhari ya yi murabus ko sojoji suyi juyin mulki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel