Hukumar zabe na zargin wani gwamna da laifin rijistar zabe sau biyu

Hukumar zabe na zargin wani gwamna da laifin rijistar zabe sau biyu

- Hukumar zaben ta kasa wato INEC ta zargi gwamnan jihar Kogi da yin rijistar zabe sau biyu bayan rijistar da ya yi a shekarar 2011 a birnin tarayya Abuja

- Hukumar tace ta soke rijista na biyun da gwamnan ya yi

- Mai magana da yawun gwamnan ya ce gwamna ya shiga wani yanayin da ya tilasta masa sake rijistan ne bayan kokarin mayar da rijistarsa ta farko Kogi daga Abuja

Hukumar zaben mai zaman kanta wato INEC a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu ta sanar cewa ta nesanta kanta daga sake rijistar katin zaben da gwamna Yahaya Bello na jihar Kogin ya yi a ranar 23 ga watan Mayu a fadar gwamnatin jihar da ke Lokoja bayan rijistar da ya yi a shekarar 2011 a unguwar Wuse da ke birnin Abuja.

Sanarwar ta ce hukumar tana da cibiyar rijista daya a ko wacce karamar hukumar kasar domin aikin cigaba da masu yin zabe rijista, tana mai cewar yi wa gwaman rijista a fadar gwamnatin jihar Kogi da ke lokoja ya saba wa doka.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, hukumar ta ce kashin na farko a karamin shashi na daya karkashin sashi na 308, na kundin tsarin mulkin kasar ne ya hanata gurfanar da gwamnan a gaban kotu.

Hukumar zabe na zargin wani gwamna da laifin rijistar zabe sau biyu

Hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa ta ce har yanzu tana tare da katin zaben wasu 'yan Najeriya

Amman duk da haka ta soke rijista na biyun da gwamnan ya yi, kuma za ta dauki matakan ladabtarwa kan jami'inta da ya sake yi wa gwamnan rijista sabanin tsarin hukumar.

Tun ranar 23 ga watan ne wata kungiya mai suna Kogi for Change ta yi barazanar kai gwaman kotu tana mai cewar laifi ne yin rijistan zabe sau biyu.

KU KARANTA KUMA: Sule Lamido ya daura daramar yakin neman zaben shugaban kasa

Rahotanni daga kafafan yada labarai sun ambato Mista Kingsley Banwo yana cewar gwamna ya shiga wani yanayin da ya tilasta masa sake rijistan ne bayan kokarin mayar da rijistarsa ta farko Kogi daga Abuja ya ci tura.

Matsalar yin rijista fiye da daya na daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga samun sashihin zabe a kasar. Wannan na daga cikin dalilan da ya sa aka fara amfani da na'urar tantance masu zabe a zaben shekarar 2015.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani dan jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel