Nan da watanni 3 Najeriya zata fita daga koma bayan tattalin arziki – Inji El-Rufai

Nan da watanni 3 Najeriya zata fita daga koma bayan tattalin arziki – Inji El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce kasar Najeriya zata kubuce daga karayar tattalin arziki

- El-Rufai ya ce a halin yanzu fannin noma da masana’antu sun bunkasa

- Gwamnan jihar Katsina ya ce bana ba za a samu cikas ta bangaren taki ba kuma zai wadata

Gwamnatin tarayya ta nuna kwarin gwiwa nan da watan Agusta kasar zata fita daga karayar tattalin arziki wanda ya fito fili sakamakon faduwar gangar man fetur a duniya.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, biyo bayan taron majalisar tattalin arzikin Najeriya ta kasa. Daya daga cikin ‘yan kwamitin, gwamna Nasiru El-Rufai, yace cikin wata uku masu zuwa in Allah ya yarda Najeriya zata fita daga cikin halin kaka na kayi na tattalin arzikin kasar.

Gwamna El-Rufai ya ce: “Yanzu haka fannin noma da masana’antu sun bunkasa, amma fannin mai shine ya sauka, tun da ‘yan tsagerun yankin Niger-Delta sun daina barnata bututun mai cikin watanni uku za a fita daga karayar tattalin arziki a Najeriya.

Nan da watanni 3 Najeriya zata fita daga koma bayan tattalin arziki – Inji El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai

Ga lamuran noma gwamna Aminu Masari, ya ce bana ba za a samu cikas ta bangaren taki ba, inda yace bana taki zai wadata.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da Litinin a matsayin ranar hutu

Masana lamuran tattalin arziki da kudi irinsu kwamishinan kudi na Gombe, Hassan Mohammad, na yabawa komawa zabin noma da gwamnatin tarayya ta yi baya ga man fetur.

Shima mai sharhi ta yanar gizo kwamrad Baban Sharif Gumel, ya ce hana shigo da abinci cikin Najeriya daga ketare yayi fa’ida.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari a'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel