Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da Litinin a matsayin ranar hutu

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da Litinin a matsayin ranar hutu

- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin bikin ranar demokradiyya

- Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Litinin, 29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin bikin ranar demokradiyya.

Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja.

Ministan ya taya ‘yan Najeriya murnar sake zagayowar ranar Demokradiya, wanda hakan yayi daidai da cikar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari shekaru biyu a kan mulki.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta kama Messi da mahaifin sa da babban laifi

‎ Mallam Dambazau ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da cewa gwamnati na ci gaba da kokari gurin ganin ta cimma manufofinta guda ukku da suka hada da tsaro, daidaita tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya yi ma dukkan yan Najeriya fatan yin bikin demokradiya cikin farin ciki da annashuwa sannan kuma ya bukace su da su hada hannu tare da gwamnati gurin gina zaman lafiya da kuma dorewar manufar damokradiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel