Wani Fasto ya damfari matar Atiku naira miliyan 918

Wani Fasto ya damfari matar Atiku naira miliyan 918

- Uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ta yi roko a gaban babban kotu da ke Legas da, ta taimaka ta kwato mata hakkin ta, a hannun wani fasto

- Ta dauki amanar kudi har naira miliyan 918 ta damka masa, a matsayin za su yi kasuwanci

Uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ta yi roko a gaban alkalin babban kotun Ikeja da ke Legas cewa, ta taimaka ta kwato mata hakkin ta, a hannun wani fasto wanda da dauki amanar kudi har naira miliyan 918 ta damka masa, a matsayin za su yi kasuwanci.

"A tunani na ba zai taba cuta ta ba tunda na ga ce3wa shi babban malamin kirista ne wannan ne ya sa na dauki amanar dukiyata na damka masa. Ban taba tunanin zai cutar dani ba saboda yawan ambaton Allah dake bakin sa."

Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito cewa Titi Abubakar ce da bakinta ta bayyana wa kotun haka a yayinda take amsa tambayoyi dangane da abin da ta sani a kan tuhumar Fasto Nsikak Abasi Akpan-Jacobs, Abdulmaliki Ibrahim da kuma Dana Motors, Ltd.

KU KARANTA KUMA: Za’a ci gaba da bincikar sarkin Kano

Hukumar dake yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC ce ta gurfanar da su, inda ake zargin su da cin amana, zamba da kuma sata gami da yi wa dukiyar wani hankaka-maida-dan-wani-naka, har na zunzurutun kudi naira milyan 918, mallakar kamfanin THA Shipping Maritime Services Ltd, na matar Atiku.

Lauyan Faston da ake kara, ya yi kokarin yi wa Titi asarkala a gaban alkali, inda a lokacin da ya ke yi mata tambayoyi, ya kalubalance ta dangabe da yadda ta yi amfani da sunaye daban daban a wasu takardun kamfani da harkokin kudi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kamfanin THA Maritime din mallakar ita Titi da Fasto Akpan ne sai kuma wani mai suna Fred Hilmes. An dai kafa kamfanin a cikin 2000.

An tsara cewa Titi ke da kashi 49 na hannun jari, yayin da Akpan da Holmes kowa kashi 25. Daga baya sai Fasto ya zagaye ya sake sabon kasafi, inda ya bai wa kan sa kashi 70, Titi da Holmes kuwa kowa kashi 15. Ya kuma sake wa kamfanin sabuwar rajista, a matsayin kuma shi ne Babban Manajan Darakta.

Daga inda Fasto Akpan ya fara daukar Dala da gammo, shi ne yadda ya saida kamfanin kacokan ga Dana Motors a kan kudi naira milyan 918, kamar yadda EFCC suka gabatar wa kotu rubutattun shaidu tabbatar wannan cinikin biri a sama da aka yi a tsakanin Akpan da Dana Motors.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta kama Messi da mahaifin sa da babban laifi

Wannan kamfani dai ya na a kan Titin Oshodi-Apapa, a rukunin masana’antu na Amuwo-Odofin, mai lamba C63A.

Da ake kora bayanai a gaban alkali, lauyan Fasto Akpan ya musanta ikirarin da Titi tayi na cewa ta zuba jari ya kai na naira bilyan 1.2.

A haka dai aka yi ta musayar kalamai, har lauyan EFCC ya sa baki inda ya rika kawo hujjojin rashin gaskiyar Akpan. Bayan kuma ita ma Titi ta bayyana yadda kudin da ta zuba su ka kai naira biliyan 1.2

An dai daga karar sai 5 da 6 ga Yuli, kuma alkali ya ci Akpan tarar Naira dubu 100 saboda jan-kafa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko http://twitter.com/naijcomhausa

Mutanen Najeriya na koka halin da ake ciki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel