Bayan majalisar dattawa ta amince da dokan kamfanin man fetur, za’a shafe NNPC

Bayan majalisar dattawa ta amince da dokan kamfanin man fetur, za’a shafe NNPC

A yau ne Alhamis, 25 ga watan Mayu, majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da dokan kamfanin man fetur bayan shekaru 17 tana zauna.

Wannan doka zai wajabta shafe kamfanin NNPC amma za’a samar da wasu sabbin ma’aikatu a madadinta.

Daga ciki shine sabon ma’aikatar kula da man feturin Najeria, wato Nigerian Petroleum Regulatory Commission (NPRC).

Hukumar lura da farashin man fetur wato Petroleum Product Pricing Regulatory Agency (PPPRA) na karkashinta.

Bayan shekaru 17, majalisar dattawa ta tabbatar da dokan kamfanin man fetur kuma za’a shafe NNPC

Bayan shekaru 17, majalisar dattawa ta tabbatar da dokan kamfanin man fetur kuma za’a shafe NNPC

Na biyu shine hukumar kula da kadaran kamfanin man feturin Najeriya wato Nigerian Petroleum Asset Management Company (NPAMC) da kuma kamfanin man fetur Najeriya NPC.

KU KARANTA: Za'a fara neman wata azumin Ramadana ranar Juma'a

Idan aka rattaba hannu kuma aka zamar da ita dokar kasa, ana sa ran zai habaka sashen arzikin man Najeriya. Kana ana sa ran cewa zai rage rashawa da shirme a sashen.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel