Majalisar dattawa Najeriya ta amince da dokar albarkatun man fetur ta kasa

Majalisar dattawa Najeriya ta amince da dokar albarkatun man fetur ta kasa

- A karshe dai majalisar dattawa ta amince da dokar albarkatun man fetur da iskar gas ta kasa

- Shugaban majalisar dattawan ya yabawa ‘yan majalisar na amincewa da suka a kan kudurin

- Yanzu haka sauran majalisar wakilai ita ma ta amince da kudurin

Majalisar tattawan Najeriya ta amince da kudurin dokar yin sauye-sauye ga dokokin sarrafa mai da iskar gas a kasar wato Petroleum Industry Bill.

Kwamitin hadin gwiwa da majalisar ta kafa kan man fetur da albarkatun gas ne ya gabatar da rahoton a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Bayan duba ga kudirin, tare da yin 'yan kananan sauye-sauye, majalisar ta amince da kudurin, inda ya kusa zama doka.

Majalisar dattawa Najeriya ta amince da dokar albarkatun man fetur ta kasa

Majalisar dattawa ta amince da kudurin dokar yin sauye-sauye ga dokokin sarrafa mai da iskar gas

An shafe shekaru ba a amince da kudurin ba saboda hakan ba zai rasa nasaba da fatan da ake da shi na kawo sauye-sauye a bangaren man fetur da iskar gas na kasa.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin BBC cewa shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki ya ce: " Ina yi wa majalisar dattawa murna na amincewa da suka yi da wannan kuduri wanda ya dade a majalisar.”

Kuduri ne da yake son kawo sauye-sauye kan yadda ake gudanar da al'amura a bangaren man fetur, da kuma kawo sauye-sauye a kamfanin mai na kasa NNPC, ta yadda kamfanin zai dinga gogayya da manyan kamfanonin mai na duniya domin samun riba maimakon faduwar da yake yi wanda ake ganin zargin cin hanci da rashawa da ya adabi kasar ne ya jawo hakan.

KU KARANTA KUMA: Jaruman da suka fara yakin Biyafara a Najeriya sun kasance masu butulci – Obasanjo

Ainihin kudurin ya zo ne daga bangaren zartarwa, amma amincewar na yanzu ya zo ne daga bangaren 'yan majalisa wato yunkurinsu ne na ganin an kawo sauyi a wannan fanni shi yasa aka zo wannan gaba.

Sai dai har yanzu da sauran tafiya domin akwai bukatar majalisar wakilai ita ma ta amince da wannan kuduri sanan kuma a aika shi zuwa fadar shugaban kasa kafin daga bisani ya zama doka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel