Ana samun raguwar cutan kanjamau a Kaduna

Ana samun raguwar cutan kanjamau a Kaduna

- Hukumomi a jihar Kaduna sun ce ana samun raguwar yaduwar cutar

- Rahotanni sun nuna cewa an kwashe shekaru ana yaki da cutar a jihohin kasar

- A shekarun baya, alkalumman da hukumar hana yaduwar cutar HIV/AIDS ta Najeriya (NACA) ta fitar sun nuna cewar jihar ta Kaduna ta zo ta uku a jerin jihohin da ke gaba-gaba a sahun jihohin da cutar ta fi kamari a kasar

Hukumomi a jihar Kaduna sun ce ana samun raguwar yaduwar cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki.

An dai kwashe shekaru ana yaki da cutar a jihohin kasar,musamman wadanda ake gani na gaba gaba wajen yawan masu dauke da cutar.

A shekarun baya, alkalumman da hukumar hana yaduwar cutar HIV/AIDS ta Najeriya (NACA) ta fitar sun nuna cewar jihar ta Kaduna ta zo ta uku a jerin jihohin da ke gaba-gaba a sahun jihohin da cutar ta fi kamari a Najeriya inda yawan sabbin masu kamuwa da cutar a ko wacce shekara a jihar ya kai kashi 9.2%, amman yanzu bai kashi 2 cikin 100 (2%) ba.

Ana samun raguwar cutan kanjamau a Kaduna

Ana samun raguwar cutan kanjamau a Kaduna

kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Paul Manya Dogo, ya ce yanzu gwamnatin jihar tana neman yaduwar cutar ta ragu zuwa kasa da 1%.

Hukumomin lafiya dai a jihar na daukar matakai da suka hada da gwaji domin gano masu dauke da cutar tun da wuri, da kuma gwajin mata masu juna biyu domin hana yaduwar cutar ga jarirai da kuma bada magunguna ga wadanda suka riga suka kamu da cutar.

KU KARANTA KUMA: Jaruman da suka fara yakin Biyafara a Najeriya sun kasance masu butulci – Obasanjo

Dokta Paul Manya Dogo ya ce hukumomi jihar suna kokarin wanzar da shirin yaki da cutar har bayan kungiyoyi masu ba da tallafi a shirin sun tafi.

Ya ce ana kokarin ne ta hanyar samar da kasafin kudi ga shirin yaki da yaduwar cutar HIV/AIDS da kuma da horar da ma'aikatan gwamnati da kuma tabbatar da cewar wata hukumar gwamanti za ta iya ci gaba shirin bayan kungiyoyin masu zama da kansu sun tafi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel