Sule Lamido ya daura daramar yakin neman zaben shugaban kasa

Sule Lamido ya daura daramar yakin neman zaben shugaban kasa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya daura daraman yakin neman zaben kujeran shugaban kasan Najeriya a shekarar 2019 ana saura shekara 2.

Lamido ya bayyana hakan ne a ranan Litinin, 22 ga watan Mayu a wata taron shugabannin jam’iyyar Peoples Democractic Party (PDP) 36 a babban birnin tarayya Abuja.

Anyi wannan ganawa ne a wata katafaren gida dake unguwan Maitama a Abuja.

Bayanin Lamido ya zo ne misalin makonni biyu bayan an bashi beli akan laifin yin maganganu masu iya tayar da rikici wanda gwamnatin jihar Jigawa ta shigar kotu.

2019: Sule Lamido ya daura daraman yakin neman zaben shugaban kasa

2019: Sule Lamido ya daura daraman yakin neman zaben shugaban kasa

Ance Lamido ya bayyana shirinsa ga shugabannin jam’iyyar na jihohin kasa ga baki daya da kuma na yankuna 6 a taron liyafar.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Sokoto ta bankado bogin ma'aikata

Daya daga cikin makusantansa ya bayyanawa jaridar Daily Sun cewa wannan kasa Najeriya tayi masa abbubuwa masu yawa kuma hanyar da zai iya biyanta shine bauta ma kasar a 2019.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel