Za’a fara neman watan Ramadan ranar Juma’a – Inji Sultan

Za’a fara neman watan Ramadan ranar Juma’a – Inji Sultan

Mai alfarma Sarkin Musulmai, kuma shugaban majalisar koli ta malamai, NSCIA Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bukaci musulman kasar nan dasu fara neman jinjirin watan Ramadan a ranar Jama’a.

Daraktan sha’anin mulki na NSCIA, Ustaz Isa Christian Okonkwo ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 24 ga watan Mayu, inda ya taya al’umman musulmai murnan karasowar watan Ramadan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Duk sojan da aka kama da hannu a yunkurin juyin mulki tasa ta kare - Inji Janar Buratai

“Tun bayan azumin shekarar data gabata, kwamitin neman watan ta shawarci mai alfarma Sarkin Musulmai dangane da ganin wata da a dinga fitar da sanarwar ganin wata a kowanne wata. Don haka ne Sultan ya shawarci musulmai dasu fita neman ganin wata a ranar 26 ga watan Mayu, wanda yayi daidai da 29 ga watan Sha’aban.” Inji Ustaz Okonkwo

Za’a fara neman watan Ramadan ranar Juma’a – Inji Sultan

Jinjirin wata

Sultan yace muddin an ga watan a daren Juma’a, jama’a su taimaka su sanar da sarakunan al’umma, don a sanar da ranar Asabar a matsayin daya ga watan Ramadan, idan kuma ba’a gani ba, Lahadi 28 ga watan Mayu ya zama daya ga watan Ramadan 1438 bayan hijra.

Daga karshe sanarwar ta kara da shawartan musulmai dasu jajirce wajen ribatan watan Azumin Ramadan, sa’annan majiyar NAIJ.com ta ruwaito an bada lambobin wayan daya kamata a tuntuba domin sanar da ganin jinjirin watan kamar haka.

Mallam Hafiz Wali 08036009090

Shaykh Tahir Bauchi 08032103733, 08033058201

Shaykh Kariballah Kabara 08035537382

Muhammad Nasir AbdulMuhyi 08065687545, 08024333381

Shaykh Habeebullahi Adam Abdullahi Al-Ilory 08023126335

Alhaji Abdul Hamid Oyebode 08037063923

Prof. Z I Oboh Oseni 08033574431

Shaykh AbdurRahman Ahmad 08023141752.

Malam Simwal Usman Jibrin 08033140010

Alhaji Yusuf Nwoha 08030966956

Sheik Bala Lau 08037008805

Sheik Sani Yahaya Jingir 08065687545

Sheik Adam Idoko 08036759892

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayin yan Najeriya game da satar amsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel