Buhari na kara samun sauki kwarai – Ofishin jakadanci

Buhari na kara samun sauki kwarai – Ofishin jakadanci

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara samun sauki sosai a birnin Landan

- Wata majiya daga ofishin jakadancin Landan ta bayyana cewa shugaban kasar na samun sauki sosai da sosai

- Majiyar ofishin jakadancin ya ce shugaban kasar na cikin kyakkyawan hali kuma yana salolin sa guda biyar a kullun

Wata majiya ce a Ofishin Jakadancin Najeriya a Landan ta bayyana cewa Buhari na samun sauki kwarai da gaske.

A halin yanzu Shugaba Muhammadu Buhari ya na samun sauki sosai duk da dai likitocin sa ne kadai za su iya bayyana ranar da ya dace ya koma Najeriya.

“Mun gode wa Allah, domin shugaban kasa ya warware sosai, kuma ya kara samun kuzari, to amma likitocin sa ne kadai za su iya bayyana lokacin da ya kamata ya koma Nijeriya.”

A cewar majiyarmu kuma jami'in da ke zuwa wajen Buhari a kullum, ya nemi a sakaya sunan sa, domin ya ce ba shi da hurumin da zai yi magana da ‘yan jarida.

Buhari na kara samun sauki kwarai – Ofishin jakadanci

Wata majiya daga Ofishin jakadancin Najeriya a Landan ta bayyana cewa Buhari na kara samun sauki kwarai

KU KARANTA KUMA: Jaruman da suka fara yakin Biyafara a Najeriya sun kasance masu butulci – Obasanjo

NAIJ.com ta tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kasar nan ranar Lahadi 7 ga Mayu, 2017 domin ci gaba da duba lafiyar sa a Landan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kun goyi bayan juyin mulki a Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel