Giyan mulki na buga ka - Falana yayi kaca-kaca da Garba Shehu

Giyan mulki na buga ka - Falana yayi kaca-kaca da Garba Shehu

Lauya kuma mai yakin kare hakkin Dan Adam, Femi Falana ya siffanta jawabin Mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu akan tsare El Zakzaky a matsayin zalunci.

Yayinda yake magana da manema labarai a ranan Talata, Shehu yace El Zakzaky duk da cewan kotu tace a sake El Zakzaky, ana kula dashi a tsare.

Amma a wata jawabin na Femi Falana a ranan Laraba, yayiwa Shehu raddi da cewa giyan mulki na buga sa.

“A wata maganar banza da mai magana da yawun Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jiya na nuna halalcin cigava da tsare El Zakzaky da uwargidansa, Ibraheema El Zakzaky.

Giyan mulki na buga ka - Falana yayi kaca-kaca da Garba Shehu

Giyan mulki na buga ka - Falana yayi kaca-kaca da Garba Shehu

“Shehu yayi ikirarin cewa duk da cewa umurnin kotu na ranan 2 ga watan Disamba, 2016, gwamnatin tarayya ba zata sake shi ba saboda wani dalilin yaudara na cewa ana kula da shi kuma an rike uwargidansa ne saboda tana kula da shi.

“Game da cewan Shehu, ana cigaba da tsare El Zakzaky ne saboda amfanin kanshi, idan aka sake shi, me kuke tunanin zai faru a gari? Ba wai an rikeshi a matsayin firsuna ba ne. Yana tare da iyalansa, idan suna bukatan wucewa su wuce. "

KU KARANTA: Babu cin mutuncin da ya wuce juyin mulki - Buratai

A tarihin Najeriya, wannan shine lokaci na farko da gwamnatin demokradiyya zata zata fito fili ta tsare mutum sabanin umurnin kotu."

“Ko a gwamnatin sojan Buhari/Idiagbon, umurnin kotu na cewa a saki wadansu da aka tsare, anyi biyayya."

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad

Dandalin Kannywood: Zan so diyar ciki na tayi harkar fim - Sadiq Ahmad
NAIJ.com
Mailfire view pixel