Na shiga ban ɗauka ba: An kama ɗaruruwan baƙin haure a jihar Edo

Na shiga ban ɗauka ba: An kama ɗaruruwan baƙin haure a jihar Edo

- Hukumar kula da shige da fice ciki da wajen kasar nan ta kama baƙin haure 400 a Edo

- Hukumar tace tace ta samu bayanan sirri dake nuna karuwar bakin hauren ne

Sama da bakin haure 400 hukumar kula da shige da fice ta kama a jihar Edo da laifin shigowa Najeriya ba tare da ka’ida ba, wanda hakan yayi karo da dokokin kasa.

NAIJ.com ta samu rahotannin dake nuna da misalin karfe 4 na daren ranar Laraba ne hukumar kula da shige da fice ta fara wani samame a dukkanin kananan hukumomin jihar Edo guda 18.

KU KARANTA: An kama ɗalibai 32, 8 sun jikkata sakamakon rikicin zaɓe a kwalejin Ilimi

Hukumar ta bayyana cewar wasu daga cikin bakin hauren data kama a kananan hukumomin Oredo, Ikpoba-Okha, Esan-West da Uhunmwode sun kutso kai Najeriya ne daga kasashen Nijar, Mali da Chadi.

Na shiga ban ɗauka ba: An kama ɗaruruwan baƙin haure a jihar Edo

Daruruwan baƙin haure

Babban kwamandan hukumar na jihar Edo, David Adi ya tabbatar da kamen, inda yace sun gudanar da samamen ne bayan samun rahoton sirri da suka wanda ke nuna yawan bakin haure na kara hauhawa.

Adi yace duk da cewa yayan kasashen yammacin Afirka nada ikon shiga kowanne kasa a yankin, amma ya zama wajibi su mallaki takardun da suka dace. Sai dai Adi ya tabbatar da wasu daga cikin jami’an su sun samu raunuka yayin gudanar da kamen.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tsadar rayuwa, yan Najeriya sun koka

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel