An kama ɗalibai 32, 8 sun jikkata sakamakon rikicin zaɓe a kwalejin Ilimi

An kama ɗalibai 32, 8 sun jikkata sakamakon rikicin zaɓe a kwalejin Ilimi

- Rikicin kabilanci ya barke sakamakon dage zaben shuwagabannin dalibai a Bauchi

- An tabbatar da dalibai guda takwas sun samu munanan raunuka

Rundunar Yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da dalibai guda takwas sun samu munanan raunuka biyo bayan wani rikicin daya kaure a kwalejin Ilimi na jihar sakamakon zaben shuwagabannin dalibai.

Kaakakin yansandan jihar garin ne ya bayyana haka, inda yace daliban kwalejin Ilimi dake garin Kangere su takwasa sun jikkata yayin da aka kacame da rikicin tsakaninsu, inda yace rikicin nada nasaba da kabilanci da addini.

KU KARANTA: Anyi ma wani malami ɗan Najeriya kyautan N12,000,000 a kasar Birtaniya

“Biyo bayan daga zaben da aka yi, sai wasu daruruwan miyagun mutane daga kauyukan gefen makarantar suka tare hanyar Bauchi zuwa Gombe suka dinga tare mutane sun cin mutuncin su” inji Kaakakin yansandan, Haruna Mohammed.

An kama ɗalibai 32, 8 sun jikkata sakamakon rikicin zaɓe a kwalejin Ilimi

Yansanda

NAIJ.com ta ruwaito sanarwar hukumar yansandan kamar haka:

“Da misalin karfe 2 na ranar Laraba 24 ga watan Mayu yayin gudanar da zaben shuwagabannin daliban kwalejin Ilimi dake Kangere ne rikicin kabilanci da na addini ya kaure tsakanin daliban, wanda hakan yayi sanadiyyar dage zaben

“Bayan hakan ne wasu miyagun mutane suka afka kan titi, suka tare hanyar Bauchi zuwa Gombe, sai dai kafin zuwan yansanda, sojoji sun tarwatsa su, sun kama mutane 32. A yanzu haka an girke motocin yansanda don tabbatar da tsaro a yankin.

“Sai dai an samu mutane 8 da suka jikkata, kuma an garzaya dasu babban asibitin jihar Bauchi don basu kulawa, su kuma wadanda aka kama zamu mika su gaban kuliya bayan kammala bincike.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hanyoyin rage kiba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel