Fargabar tashin hankali a jihar Osun, gwamnati ta baza jami'an tsaro

Fargabar tashin hankali a jihar Osun, gwamnati ta baza jami'an tsaro

- Ana fargabar wasu samari suna so su dauki doka a hannunsu a jihar Osun, amma Gwamnati ta baza jami'an tsaro domin kame masu son tada zaune tsaye a gari

- Jiya Laraba wasu dalibai sunyi muzahara a jihar

- Gwamnati ta gargadi masu son tada fitina

Ana fargabar wasu samari suna so su dauki doka a hannunsu a jihar Osun, amma gwamnati ta baza jami'an tsaro domin kame masu son tada zaune tsaye a gari. An kuma bada umarnin kame duk wanda ya dauki doka a hannunsa.

Fargabar Tashin Hankali a jihar Osun, Gwamnati Ta baza Jami'an Tsaro

Fargabar Tashin Hankali a jihar Osun, Gwamnati Ta baza Jami'an Tsaro

Sanarwar da gwamnati ta fitar a babban birnin jihar Osun shine cewa duk wanda ya fito domin tada rigima, a kame shi a rufe, a kokarin ta na dakile sabuwar rigima da wasu zauna-gari-banza ke kokarin tayarwa.

Jiya dai laraba an sami wasu daliban da suma suka fita zanga zanga, amma majiyar tsaro tace wasu na son lallai abin ya fi haka don su sami damar sata da bizi a kan dukiyoyin al'umma, wannan lamari dai na faruwa ne a yanzu-yanzu, zamu bi muku batun don jin yadda ta kaya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel