Duk sojan da aka kama da hannu a yunkurin juyin mulki tasa ta kare - Inji Janar Buratai

Duk sojan da aka kama da hannu a yunkurin juyin mulki tasa ta kare - Inji Janar Buratai

- Buratai ya aika da muhimmin sako ga masu tunanin Juyin Mulki

- Buratai yace ba zai ci amanan shugaba Buhari ba

Jaridar Rariya ta ruwaito shugaban rundunar sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, yana bayyana cewa babu wani cin amana da ya wuce juyin mulki, ga gwamnatin dimokuradiyya.

Buratai yace cin amana ne babba ace sojoji sun hambarar da gwamnatin da talakawa suka zaba da hannunsu, Buratai ya kara da cewa abin takaici ne ace wasu tsoffin shuwagabannin kasa, da yan siyasa, suna hure kunnuwan wasu daga cikin sojoji da sunan suyi juyin mulki a kasar nan.

KU KARANTA: Toh fa: Buratai ya lashi takobin harbe duk kwamandan dake da hannu a yunkurin juyin mulki

Burati ya bayyana haka ne a wani taron da-ya hada manyan hafsoshin sojin kasar, da aka gudanar a babbar hedikwatar tsaro ta kasa dake Abuja.

Duk sojan da aka kama da hannu a yunkurin juyin mulki tasa ta kare - Inji Janar Buratai

Buratai da Buhari

"Wata kila kun manta ko waye ke kan mulki, kuma wata kila kun manta ko waye ke rike da rundunar sojin kasar nan, shi ya sa har kuka yi yunkurin shirya abinda ku kanku kunsan cewa ba zai taba yiwuwa ba.

“Saboda haka ina sanar da ku cewa duk wanda ya san yana da hannun a wannan yunkuri na cin amanar kasa to ya gaggauta tonawa kansa asiri da kansa, tun kafin ni Buratai, in tona masa asirin” Inji Buratai.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Buratai yana fadin:

“Ina nan ina gudanar da bincike daya bayan daya kuma, na rantse da wanda ya halicceni, da hannuna zan sa bindiga, in harbe, duk wanda na samu da hannun a wannan cin amana da aka so yiwa gwamnatin mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari"

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Meke kawo matsalar satar amsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel