Buratai ga ýan Najeriya - “Ku daina yarda da jita jitan juyin mulki”

Buratai ga ýan Najeriya - “Ku daina yarda da jita jitan juyin mulki”

- Laftanar janar Buratai ya shawarci yan Najeriya su daina yada jita jitan juyin mulki

- A makon daya gabata ne aka dinga rade raden juyin mulki a Najeriya

Hukumomin dakarun sojin Najeriya sun yi kira ga 'yan Najeriya da suyi watsi da rahotannin da ake yadawa na jita-jitar yiwuwar juyin mulki, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Shalkwatar tsaro ta sojojin Najeriya ce ta fitar da wata sanarwa inda take sukar jita-jitar da wasu ke bazawa na yiwuwar juyin mulki a kasar.

KU KARANTA: Mabiya addinin Shi’a sun gindaya ma gwamnati matakan yin sulhu

Jita jitan juyin mulkin ya samu asali ne tun bayan sauyin aiki da babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai yayi wa manyan hafsoshin sojin kasar ne, kamar yadda NAIJ.com ta binciko.

Buratai ga ýan Najeriya - “Ku daina yarda da jita jitan juyin mulki”

Buratai

Cikin sanarwar da kakakin shalkwatar tsaro ta sojojin Najeriya, Manjo-Janar John Enenche, ya fitar, ya tabbatar da cewa babu wani dalilin da zai sa 'yan Najeriya su damu, yace sojojin kasar suna bai wa mulkin dimokradiyya cikakken goyon baya a kasar.

Eneche ya kara da cewa bayanan babban hafsan sojojin kasar game da dangantakar da ke tsakanin wasu fararen hula da sojoji abu ne da aka saba yi domin jan kunnen sojojin, kuma domin su tabbata ba su kauce wa tsarin aikinsu ba.

Tun bayan fitar jita jitar, manyan 'yan siyasa da masu kare radin dimokradiya sun yi kiraye-kiraye da a gabatar da bincike kwakwaf don gano masu hannu cikin kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Ita ma a nata bangaren fadar gwamnatin kasar, ta bakin Kaakain Buhari, Femi Adesina, ya yi kira ga 'yan kasar da kar su yarda da wannan rade-radi don ba gaskiya ba ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Su wanene ke son Buhari yayi murabus?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel