Hukumar yansanda zata yaye rukunin farko na Yansanda 10,000

Hukumar yansanda zata yaye rukunin farko na Yansanda 10,000

- Yansanda sama da 200 cikin dubu goma da aka dauka sun kammala samun horo

- Hukumar yansandan Najeriya zata yaye rukunin yansanda na farko daga cikin 10,000

Za’a yaye rukunin farko daga cikin yansanda 10,000 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka daga kwalejin horar da yansanda na jihar Legas.

Kwamandan kwalejin, Boniface Onyeabor ya fada ma kamfanin dillancin labaru, NAN a ranar Laraba 34 ga watan Mayu inda yace Yansanda 123 masu mukamin Sufeto da kurata 52 ne suka kammala samun horo.

KU KARANTA: Mabiya addinin Shi’a sun gindaya ma gwamnati matakan yin sulhu

A ranar 15 ga watan Agusta ne NAIJ.com ta ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin yansanda 10,000 don kara yawan jami’an yansandan Najeriya.

Hukumar yansanda zata yaye rukunin farko na Yansanda 10,000

Yansanda

“Rukunin farko na yansandan da suka samu horo sun fita a ranar 19 ga watan Mayu, za’a basu hutun sati 2 kafin su fara aiki.” Inji shi.

Onyeabor ya kara da cewa kimanin yansanda 1300 ne zasu kammala samun horo daga wannan watan zuwa watan Disamba, sa’annan ya kara da cewa an basu horon daya dace da zamani.

Onyeabor, wanda ya kai mukamin kwamishinan yansanda yace an horar da yansandan don su kasance masu kare hakkin dan adam, yaki da rashawa, da dukkanin wasu miyagun laifuka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kuna goyon bayan Buhari yayi murabus?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel