Gwamnati ta kafa kwamitin mutane 29 da zasu sasantawa karin albashi

Gwamnati ta kafa kwamitin mutane 29 da zasu sasantawa karin albashi

- Gwamnatin tarayya ta kafa wata kwamitin da zasu tattauna da kungiyoyin ma’aikata kan batun karin albashi mafi karancin na naira 56,000

- Ministan kwadago ya ce gwamnati ta kafa kwamitin ne don ya jawo kungiyoyi na kwadago da nufin kaucewar rikici tsakanin gwamnati da kungiyoyin ma’aikatan.

- Sabuwar kiddidigar na nuna tattalin arzikin kasar ya ragu da kusan rabin kashi a zangon farko na shekarar bana

A rikicin da ke tsakanin gwamnatocin tarrayar Najeriya da ma’aikatan kasar, gwamnatin kasar ta kafa wani kwamitin mutane 29 da ta dorawa alhakin tattauna batun sabon karin albashin ma’aikata a kasar.

Tun a cikin watan Mayun bara ne dai ma'aikatan kasar suka mika wata bukatar karin albashin da ya kai na kusan naira 56,000 ga gwamnatin da nufin rage radadin janye talafin man fetur a kasar. An dai dauki lokaci ana tattaunawa a tsakanin ma'aikata da gwamnatin kafin mika wani rahoto ga gwamnatin kasar a cikin watan Afrilun da ya shude.

A ranar Laraba, 24 ga watan Mayu ne dai gwamnatin tarayyar ta fitar da wani kwamiti na mutane 29 da zai kunshi wakilai guda 5 daga bangare na gwamnatin tarrayar, sannan kuma da gwamnonin kasar guda 6 game da wakilan kungiyoyi na kwadago 8 sannan kuma da kungiyar masana'an tu da samar da aikin yi ta NECA da ita ma aka dorawa alhakin samar da wakilan guda 8.

Gwamnati ta kafa kwamitin mutane 29 da zasu sasantawa karin albashi

Kungiyoyin ma’aikatan Najeriya

NAIJ.com ta ruwaito cewa, ministan kwadago, Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnati ta yanke hukuncin jawo kowa da nufin kaucewar rikici tsakanin gwamnati da kungiyoyi na kwadago a kasar.

Ministan ya ce: “ A lokacin da zababbun ‘yan kwamitin suka hadu , muna san rantsar dasu a kwanan nan, ‘yan kwadago zasu mika bukatarsu ta naira 56,000 a matsayin mafi karancin albashi domin tattaunawa da bangarori kamar yadda doka ta kwadago a kasar ta aiyyana. A lokacin kuma masu biyan albashin zasu fadi abun da suke iya biya. Alal misali, kungiya ta masu daukar aiki ta ce ba zata iya biyan sabon albashin ba saboda hakan na nufin karin albashi har ya zuwa sama, wannan tattaunawa za'a yi ta ne a teburin tattaunawa.”

KU KARANTA KUMA: Kudin da ke cikin asusun Najeriya na tsotsewa

Ko ya zuwa yaushe ne bangarorin ke iya kaiwa ga amincewar da ta kai ga sabon albashin dai, tattaunawar ta na zuwa ne a dai dai lokacin da tattalin arzikin tarrayar Najeriyar ke nuna alamun farfadowa.

Gwamnati dai ta ce ta gamsu da wata sabuwar kiddidigar da ke fadin tattalin arzikin kasar ya ragu da kusan rabin kashi a zangon farko na shekarar bana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel