Kotu ta baiwa tsohon shugaban NNPC, Yakubu daman zuwa duba lafiyarsa

Kotu ta baiwa tsohon shugaban NNPC, Yakubu daman zuwa duba lafiyarsa

- Babbar kotun birnin tarayya ta bada umarni ga Andrew Yakubu da yaje ya duba lafiyarsa

- Alkalin kotun ya bashi sati uku don ya je ya duba lafiyarsa a Ingila

Alkalin babban kotun tarayya dake Abuja, Mai shari’a A.R Mohammed ya baiwa tsohon shugaban hukumar matan mai ta kasa, NNPC, Andrew Yakubu izinin fita kasar waje don a duba lafiyarsa.

Andrew Yakubu, ta bakin lauyansa, Ahmed Raji ya bukaci izinin kotu domin ya tafi kasar Ingila don likitoci su duba lafiyarsa, da haka ne alkalin yace:

“Tun da lauya mai kara bai musanta bukatar lauyan wanda ake kara ba, don haka na bashi daman fita ya duba lafiyarsa.”

KU KARANTA: Jami’an yansanda sun kama matasa dake yin basaja a kayan Sarki suna damfara

Haka zalika, Alkalin ya bukaci akawun kotu ya mika ma Andrew Yakubu fasfonsa na fita kasashen waje, kuma ya bashi wa’adin sati uku ne don ya kammala neman lafiyarsa na sa.

Kotu ta baiwa tsohon shugaban NNPC, Yakubu daman zuwa duba lafiyarsa

Andrew Yakubu a kotu

“Wanda ake kara zai dawo bayan sati uku, kuma daya daga cikin wadanda suka tsaya masa zai kawo takardar rantsuwa, saboda idan wanda ake kara ya ki dawowa, shi za’a kamam haka zalika zai kawo takardar rantsuwa kafin a bashi fasfon nasa, sa’annan kuma daya dawo zai dawo da fasfon kotun.”

Bayan kammala yanke hukuncin ne, daga nan sai Alkali ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Yulio.

NAIJ.com ta ruwaito a ranar 3 ag watan Feburairu na shekarar 2017 ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta bankada gidan Andrew Yakubu inda ta yi awon gaba da wasu makudan kudade daya tara a gida da suka kai $9,772,000 da £74,000.

Bayan an EFCC ta kwashe kudaden ne sai Yakubu ya amsa mallakan kudaden, da kuma gidan, a yanzu haka yana fuskantar tuhume tuhume guda 6.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Andrew Yakubu a kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel