An daure wasu 'yan makaranta kan yi wasikun tes da Boko Haram

An daure wasu 'yan makaranta kan yi wasikun tes da Boko Haram

- Jami’an tsaro sun daure wasu ‘yan makaranta kan laifin rashin yin tir da ayyukan ta'addanci

- An samu yaran ne bayan an samu wanin sakon tes a wayoyinsu na salula game da kungiyar masu tada kayar baya ta Boko Haram

- A wayoyin yaran an samu sakon cewa Boko Haram na daukar mutanen da suka dara shekara 14 aiki

- Gwamnatin kasar Kamaru ta hana taron manema labaran bisa barazanar da ta ce taron take wa doka da oda a kasar

Wata sanarwar da Kungiyar Amnesty International ta fitar ta ce Jami'an tsaro sama da 10 sun rufe dakin taron da ke wani otal a Yaunde, babban birnin Kamaru domin hana taron manema labarai da zai yi kira a saki 'yan makarantar da aka daure kan laifin rashin "yin tir da ayyukan ta'addanci."

An kama yaran ne bayan an samu wanin sakon tes a wayoyinsu na salula game da kungiyar masu tada kayar baya ta Boko Haram.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sakon tes din da aka samu A wayoyin 'yan makarantar dai yana raha ne kan Boko Haram da kuma wuyar samun aiki a Kamaru.

"Boko Haram na daukar mutanen da suka dara shekara 14 aiki. Sharadin daukar shi ne: Kiredit 4 a jarabawar GCE ciki har da addini," in ji sakon tes din.

Da wani malami ya gane sakon tes din, sai ya kwace wayar kuma ya sanar da 'yan sanda. An kama matasan 3, kuma aka daure su a watan Janairun shekarar 2015, inda aka daure su da sarka, in ji sanarwar kungiyar Amnesty International.

A watan Nuwamban bara ne dai aka samu matsan da laifin rashin yin tir da ayyukan ta'addanci kuma aka yi musu daurin shekra goma-goma.

Daliban da suka hada da Fomusoh Ivo Feh da Afuh Nivelle Nfor da kuma Azah Levis Gob daukaka kara bisa samun da laifin kuma a ranar 15 ga watan Yuni ne dai kotu zata saurari daukaka karansu.

KU KARANTA KUMA: Wata 'yar asalin jihar Bauchi ta yi zarra a gasar musabakar Kur'ani ta duniya (Hotuna)

Ita gwamantin kasar ta tabbatar da hana taron manema labaran bisa barazanar da ta ce taron take wa doka da oda.

Ministan sadarwar kasar, Issa Tchiroma, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters ta wayar tarho cewar idan zanga-zanga tana barazana ga doka da oda, hukumomi na ikon hana ta, kuma abun da aka yi kenan kan taron Amnesty International.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wasu yara wadanda rikicin Boko Haram ta rusa da iyayensu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel