Zaben cike gurbi: Jam'iyyar PDP ta bukaci INEC ta soke zaben mazabar Mashi/Dutsi a Katsina

Zaben cike gurbi: Jam'iyyar PDP ta bukaci INEC ta soke zaben mazabar Mashi/Dutsi a Katsina

Jam’iyyar PDP reshen jihar Katsina, ta ki amincewa da sakamakon zaben cike gurbi da aka gudunar na dan majalisar wakilai a mazabar Mashi da Dutsi.

Jam’iyyar ta ce tana bukatar hukumar zabe da ta gaggauta soke shi domin an tafka magudi, ta hanyar tauye wa mutane sama da 13,000 ‘yancin kada kuri’un su.

Shugaban jam’iyyar Alhaji Salisu Majigiri ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Katsina.

Jam’iyyar PDP, ta ce duk da cewa jama’a da dama sun fito domin jefa kuri’un su, amma ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin barazana ga dorewar dimokradiyya, tare da take hakkin dan Adam na bayyana ra’ayin sa.

Zaben cike gurbi: Jam'iyyar PDP ta bukaci INEC ta soke zaben mazabar Mashi/Dutsi a Katsina

Zaben cike gurbi: Jam'iyyar PDP ta bukaci INEC ta soke zaben mazabar Mashi/Dutsi a Katsina

KU KARANTA: Yadda Sarki Sanusi ya sha kyar a hannun hukumomin Kano

NAIJ.com ta samu labarin cewa PDP ta kuma yi zargin cewa, an yi amfani da jami’an tsaro da ‘yan daba wajen hana mutane damar jefa kuri’un su, ta na mai cewa sama da mutane 13,000 aka tauye wa ‘yancin jefa kuri’a, ta hanyar yi masu barazana da bakin bindiga baya ga fuskantar cin zarafi daga ‘yan daba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota

Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota

Yadda na saci motoci 4 cikin wata 4 - Inji wani kasurgumin barawon mota
NAIJ.com
Mailfire view pixel