Za’a ci gaba da bincikar sarkin Kano

Za’a ci gaba da bincikar sarkin Kano

- Hukumar dake sauraren koke-koke ta Jihar Kano ta ce za’a ci gaba da bincikar sarkin Kano

- Ta ce dama can dukkan takardunta na nan a ajiye saboda haka zata ci gaba da aikin ta

- A cewar hukumar ta samu umarnin Kotu data binciki fadar Sarkin har sau biyu

Bayan sanya baki da wasu masu ruwa da tsaki tare da tsofaffin Shugabannin kasar nan su kayi kan majalisar jihar Kano ta janye binciken da takeyi wa masarautar Kano da ya hada da kashe kudaden masarautar da sarki Muhammadu Sanusi II yayi ba bisa ka’ida ba.

Wata sabuwa ta sake kunno kai domin hukumar da ta fara bincike akan hakan ta ce dukda majalisar jihar ta dakatar da binciken ita zata ci gaba.

Hukumar dake sauraren koke-koke ta Jihar Kano ta ce dama can duk takardunta na nan a ajiye saboda haka zata ci gaba da aikin ta, a cewar hukumar ta samu umarnin Kotu data binciki fadar Sarkin har sau biyu.

Za’a ci gaba da bincikar sarkin Kano

Za’a ci gaba da bincikar sarkin Kano

Wani jami’i a hukumar yace tunda majalisar Kano din ta janye nata binciken akan masarautar Kano su yanzu za su iya komawa su ci gaba daga inda suke tsaya,domin bankado gaskiyar lamari.

KU KARANTA KUMA: Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo na shirin karbo bashi

Jami’in yace da ma can ba suji dadi ba da majalisar ta ce itama za ta binciki sarkin kuma hukumar tana da isassun bayanai akan yadda aka kashe kudaden masarautar bayan umarni da ta samu daga kotu har sau biyu ta ci gaba da bincike akan masarautar.

Da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho daga birnin Madina, Shugaban hukumar Muhuyi Magaji ya ce dukkan bayanan da suka samo tun farkon binciken na nan a ajiye suke babu abin da ya taba su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kun goyi bayan juyin mulki a Najeriya?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel