Wata 'yar asalin jihar Bauchi ta yi zarra a gasar musabakar Kur'ani ta duniya (Hotuna)

Wata 'yar asalin jihar Bauchi ta yi zarra a gasar musabakar Kur'ani ta duniya (Hotuna)

- Wata 'yar asalin jihar Bauchi, A'isha Musa Gale ta ci nasara a gasar musabakar Kur'ani ta duniya da aka gudanar a kasar Malesiya

- Ita A’isha din ta zo ta daya a bangaren mata a gasar masabukar Kur'ani ta kasa

- A'isha ta samu kyautar gwal da kudi

A'isha Musa Gale daga karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi ta kasance zakarar gwajin dafi a gasar musabakar Kur'ani ta duniya da aka gudanar a kasar Malesiya.

Idan ba a mance ba a gasar masabukar Kur'ani ta kasa da aka gudanar a watannin baya, A'isha ce ta zo ta daya a bangaren mata, wanda hakan ya sa aka zabe ta a matsayin wadda zata wakilci kasar Najeriya a gasar ta duniya.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, a yayin gasar musubakar ta duniya, A'isha ta samu kyautar gwal wanda kudinsa ya kai kimanin naira milyan 5, sannan kuma ta samu kudin da idan aka juya shi a kudin Najeriya ya kai kimanin naira milyan 2.

Wata 'yar asalin jihar Bauchi ta yi zarra a gasar musabakar Kur'ani ta duniya (Hotuna)

Gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar na mika lamba yabo ga A'isha Musa Gale

KU KARANTA KUMA: An gano biloniyan Najeriya yana tuka ‘babur’ zuwa gonar sa a jihar Kano (HOTUNA)

A yayin jawabin kwamitin musabakar ta duniya, sun jinjinawa gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Barista M.A Abubakar, wanda a cewar su muhimmancin da gwamnan ya baiwa harkar ilimi a jiharsa ne ya kai ga samun nasarar da yarinyar ta yi.

Wata 'yar asalin jihar Bauchi ta yi zarra a gasar musabakar Kur'ani ta duniya (Hotuna)

Gwamnan jihar Bauchi Barista M.A Abubakar, A'isha Musa Gale da 'yan kwamitin musabakar jihar Bauchi

A jawabin sa ga kwamitin musabakar jihar Bauchi, gwamna Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya jaddada mahimmancin ilimi ga al'umma.

Wata 'yar asalin jihar Bauchi ta yi zarra a gasar musabakar Kur'ani ta duniya (Hotuna)

Gwamnatin tarayya Barista M.A Abubakar da A'isha Musa Gale

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel