Zamu mayar da Kano kasaitaccen birni – Inji gwamna Ganduje

Zamu mayar da Kano kasaitaccen birni – Inji gwamna Ganduje

- Gwamnatin jihar Kano ta ce zata mayar da birnin Kano kasaitacce birnin wanda za'a kwatanta shi da sauran birane na duniya

- Gwamnatin jihar cimma yarjejeniyar da wasu kamfanoni guda 10 har da na gida wadanda suka fi karkaka ga harkar inganta sufuri da samar da makamashi

- Gwamnati zata gina hanyar jirgin kasa na zamani a cikin birnin Kano da kewaye

Gwamnatin jihar Kano a karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta cimma yarjejeniya da wasu kamfanonin kasashen waje dana cikin gida da nufin zuba jari wajen samar da ababen more rayuwa a jihar.

An dai cimma yarjejeniyar da akalla kamfanoni guda 10 wadanda suka fi karkaka ga harkar inganta sufuri da samar da makamashi.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce: "Mun ce muna son mayar da birnin Kano kasaitacce birnin wanda za'a kwatanta shi da sauran birane na duniya, kuma wannan yana bukatar abubuwa da yawa, saboda haka muka kira masu sa hannun jari kamfanoni guda 10 wasu ma har sun fara.”

Zamu mayar da Kano kasaitaccen birni – Inji gwamna Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta cimma yarjejeniyar gina hanyar jirgin kasa na zamani a cikin birnin Kano da kewaye

Jari mafi kauri ya fito ne daga hannun kamfanin Eighteen Engineering Company na kasar China, wanda ya cimma yarjejeniyar gina hanyar jirgin kasa na zamani a cikin birnin Kano da kewaye.

An dai ƙiyasta cewa aikin gina hanyar jirgin kasa na zamani zai lakume dala biliyan 1.8.

KU KARANTA KUMA: Yadda Sarkin Musulmi, Osinbajo, Dangote, IBB suka ceci Sarki Sanusi daga hannun yan majalisar dokokin jihar Kano

Kamfanin Dangote na daga cikin kamfanoni na cikin gida dake shirin zuba jari a jihar.

Direktan Kamfanin Dangote a jihar Kano, Alhaji Mansur Ahmed ya ce: "Kamfanin Dangote zai sa jari wajen bunkasa masana'atu da kuma bangaren samar da makamashi da hasken rana inda zai kashe dala miliya 150 kuma za'a kammala aikin cikin shekaru biyu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel