Majalisar Dinkin Duniya za ta taimakawa mutanen Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya za ta taimakawa mutanen Najeriya

– Majalisar Dinkin Duniya ta ware kudi domin maganin yunwa a Najeriya

– Ana fama da mawuyacin yunwa a Yankin Arewa maso gabas

– Don haka ne UN ta ware Dala Miliyan 24 domin kawo karshen matsalar

Kuna sane da cewa mutanen Arewa maso gabacin Najeriya na cikin wani hali.

Rikicin Boko Haram ya haifar da matsaloli da dama.

A dalilin haka kungiyoyin Duniya su ka shirya damarar taimakawa kasar.

Majalisar Dinkin Duniya za ta taimakawa mutanen Najeriya

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

A bana Majalisar Dinkin Duniya watau UN za ta taimakawa mutane kusan miliyan 7 da ke fama da mugun yunwa a Yankin Arewa-maso-Gabas na Najeriya. UN za ta kashe Dala Miliyan 24 a Najeriya.

KU KARANTA: An kashe mutane har uku kan N9000

Majalisar Dinkin Duniya za ta taimakawa mutanen Najeriya

Mutanen Najeriya na fama da yunwa

A cikin ‘yan shekaru masu zuwa dai UN za ta kashe kusan Dala Miliyan 80 a Najeriya domin agazawa Jama’an da ke cikin la-hau-la. Najeriya dai za ta zama cikin kasashen da aka fi ba taimako a Duniya.

Jiya kun ji cewa Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya daura damarar zama Dakta. Obasanjo na Digiri na uku a fannin ilmin addinin kirista inda ya gabatar da sharen fagen kundin sa. Obasanjo zai yi nazari ne a kan rashin cigaba da talauci a Yankin Arewa-maso-gabashin Najeriya a mahangar ilmin addinin kirista.

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Abubuwa sun tabarbare a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel