Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo na shirin karbo bashi

Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo na shirin karbo bashi

– Yayin da CBN ke kuka kan irin bashin da Gwamnati ke ci

– Mukaddashin Shugaban kasa ya aika wata takarda ga Majalisar

– Inda yake neman a amince Gwamnati ta karbo wasu bashin

Farfesa Osinbajo yana nema ya karbo bashin fiye da Dala Biliyan 1.

Tuni ya aika takarda Majalisa domin a amince da wannan batu.

Najeriya za ta karbi bashi ne a bankin Duniya.

Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo na shirin karbo bashi

Osinbajo na shirin karbowa Najeriya bashi

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na nema ya karbo bashin Dala Biliyan 1.28 daga bankin Duniya wanda yace an manta ba a rubutawa Majalisa a baya ba. Jiya ne dai Kakakin Majalisa Yakubu Dogara ya karanta takardar.

KU KARANTA: Tofa: Kudin Najeriya na kara tsotsewa

Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo na shirin karbo bashi

Mukaddashin Shugaban kasa tare da Saraki da Dogara

Osinbajo yake bayanin cewa Gwamnatin Tarayya ta kafa bankin DBN domin cigaban ‘Yan kasa wanda a cewar sa bankin Duniya da na raya kasashen Afrika da wasu bankunan ne dai su ka dafawa sabon bankin kasar.

Sai dai a jiya kun ji cewa Gwaman CBN Godwin Emefiele ya nuna jin tsoron sa wajen irin bashin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ke karbowa. A cewar Gwamnan bai kamata yanzu Gwamnati ta kara cin wani bashi ba don a wuce adadin abin da ya dace a karba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ibrahim Magu sun yi tattakin yaki da sata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel