Kudin da ke cikin asusun Najeriya na tsotsewa

Kudin da ke cikin asusun Najeriya na tsotsewa

– Kudin da ke asusun rarar mai yana ta ja kasa

– Abin da ke ciki ya koma Dala Biliyan 2.29

– A watan jiya dai yana kudan Dala Biliyan 2.49

Janar Obasanjo ne ya kirkiro asusun rarar man fetur a Najeriya.

Ana adana duk wata riba da aka samu wajen saida mai.

Yanzu haka dai kudin da ke cikin asusun na ta yin kasa.

Kudin da ke cikin asusun Najeriya na tsotsewa

Abin da ke asusun rarar mai yana ta ja kasa

Akanta-Janar na kasar nan Ahmed Idris ya bayyana cewa kudin da Najeriya ta ke da shi a cikin akawun din ta na ECA watau asusun rarar mai yana ja baya. A watan jiya Afrilu dai ana da Dala Biliyan 2.49 wanda yanzu ya koma Dala Biliyan 2.29.

KU KARANTA: Abin da ya hana a saki Dasuki-Gwamnati

Kudin da ke cikin asusun Najeriya na tsotsewa

Ministar kudi tare da Yemi Osinbajo

Ahmed Idris ya fadi wannan ne a Ranar Talata bayan an kammala wani taro da Ministar kudi inda aka bayyana abin da aka rabawa kowane mataki da Jiha na Gwamnati a wannan watan. Abin da aka samu dai ya ja baya daga na watan jiya.

Kun ji cewa Jihar Akwa-Ibom da sauran Jihohin Yankin kudu-maso-kudu su ka fi kowa samun rabo mafi tsoka a rabon da Gwamnati tayi daga farkon shekarar nan kawo yanzu. Kun san cewa ana karawa Jihohi masu mai kashi 13% na abin da aka samu daga fetur.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana jita-jitar cewa Buhari ya cika

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018

Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya tayi alkawarin kara albashin ma’aikata a 2018
NAIJ.com
Mailfire view pixel