Mutane 10 da su ka yi kutun-kutun wajen hana binciken Sarkin Kano

Mutane 10 da su ka yi kutun-kutun wajen hana binciken Sarkin Kano

– A baya an fara binciken Masarautar Kasar Kano

– Ana zargin fadar Kano da yin facaka da kudi da kuma wasu laifuffukan

– Wannan dai ba karamar barazana bace ga Sarki Sanusi II

Dama kwanaki kun ji cewa akwai kishin-kishin cire Sarki Sanusi II.

Wasu manyan mutane dai sun yi iya bakin kokarin wajen hana hakan.

A haka aka sauke kakan mai martaba Sarki a shekarar 1963.

Mutane 10 da su ka yi kutun-kutun wajen hana binciken Sarkin Kano

An dakatar da binciken da ake yi wa Sarkin Kano

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana wadanda su ka sa aka dakatar da binciken da ake yi wa Sarkin Muhammadu Sanusi II. A cewar sa akwai tsohon mai bada shawara kan harkar tsaro Janar Ali Gusau da tsofaffin shugaban kasa Janar Babangida da Abdusalami.

KU KARANTA: Yadda Sarki Sanusi I ya bar gadon sarauta

Mutane 10 da su ka yi kutun-kutun wajen hana binciken Sarkin Kano

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Aliko Dangote da Aminu Dantata su na cikin wadanda su ka roki a dakatar da binciken. Har da kuma Asiwaju Bola Tinubu da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III. Sauran sun hada Yakubu Dogara da Bukola Sarki da shi kan shi Farfesa Yemi Osinbajo.

Kwanakin baya NAIJ.com ta kawo maku cewa wasu Gwamnonin Arewa 5 su ka shiga tsakanin rikicin Sarkin Kano Sanusi II da kuma Gwamnan Jihar Dr. Abdullahi Ganduje a wani zama da aka yi a Kaduna.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Jama'a sun yarda Soji ya karbi mulki [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel