Toh fa: Buratai ya lashi takobin harbe duk kwamandan dake da hannu a yunkurin juyin mulki

Toh fa: Buratai ya lashi takobin harbe duk kwamandan dake da hannu a yunkurin juyin mulki

- Baban hafsan sojin Najeriya ya ce da hannun sa zai harbe duk sojan da aka samu da adin kai kan yunkurin juyin mulki a kasar nan

- Buratai ya ce babu cin amana da ya wuce juyin mulki ga gwamnatin dimokuradiyya wace talakawa suka zaba

- Buratai ya sake cewa duk wanda ke da hannu a yunkurin juyin mulki su gaggauta tonawa kansu asiri tun kafin ya tona masu asiri

Baban hafsan sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewa ya rantse da Allah, an harbe, duk kwamandan da samu da hannu a yunkurin juyin mulki.

Shugaban rundunar sojojin ya ce: “Babu wani cin amana da ya wuce juyin mulki ga gwamnatin dimokuradiyya, wace talakawa suka zaba da hannunsu, kuma abin takaici ne ace wasu tsoffin shugabannin kasa, da yan siyasa, su hure kunnuwan wasu daga cikin sojoji da sunan suyi juyin mulki a kasar.”

Wata kila kun manta ko waye ke kan mulki, kuma wata kila kun manta ko waye ke rike da rundunar sojin kasar nan, shiyasa har kuka yi yunkurin shirya abinda ku kanku kunsan cewa ba zai taba yiwuwa ba.

Saboda haka ina sanar da ku cewa duk wanda ya san yana da hannun a wannan yunkuri na cin amanar kasa to ya gaggauta tonawa kansa asiri da kansa, tun kafin in tona masa.

Ina nan ina gudanar da bincike daya bayan daya kuma, na rantse da wanda ya halicceni, da hannuna zan sa bindiga, in harbe, duk wanda na samu da hannun a wannan cin amana da aka so yiwa gwamnatin mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin yunkurin juyin mulki

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana hakan a wani taron da ya hada manyan hafsoshin sojin kasar, da aka gudanar a babbar hedikwatar tsaro ta kasa, da ke birnin tarayya Abuja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel