Ba addu'a ne zai kawo sauyi ba, aiki tukuru ne, inji Osinbajo

Ba addu'a ne zai kawo sauyi ba, aiki tukuru ne, inji Osinbajo

- Mukaddashin shugaban kasa yace sai fa anyi aiki tukuru sannan za'a sami yadda ake so kan batun tattalin arziki

- Ya ce koda cewa shi limamin coci ne, yasan sai anyi aiki ake gani a kasa

A tattaunawar sa da 'yan jarida bayan saka hannu akan muhimman kudirai na gwamnati, domin shawo kan matsalolin da arzikin Najeriya ke ciki, Osinbajo, yace kowa sai ya bada tasa gudunmawar, sannan za'a ga da kayu.

Ba addu'a ne zai kawo sauyi ba, aiki tukuru ne, inji Osinbajo

Ba addu'a ne zai kawo sauyi ba, aiki tukuru ne, inji Osinbajo

Ya kara da cewa, duk kasashen nan da suka yi fice bafa da zaljannu ko fatalwi suke aiki ba, a'a, zunzurutun dagewa ne da aiki da kwakwalwa ya kaisu ga haka, don haka 'yan Najeriya su shirya aiki sosai.

Shugaban, ya bayyana ayyukan gona, farfado da masana'antu, a cikin manyan kudirai da dole sai an kula dasu, kafin ace an kai gaci.

"In baku misali, muna cin shinkafa sosai, amma kuma wai sai mun shigo da ita, duk da cewa zamu iya noma ta mu ci kuma mu sayar, kai hatta Afirka ma zamu iya ciyarwa da noman da zamuyi na shinkafa." a cewarsa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel