Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin yunkurin juyin mulki

Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin yunkurin juyin mulki

- Hukumar Sojojin Najeriya ta musanta jita-jitan yunkurin juyin mulkin da wasu ke cewa za’a yi a kasar

- Rundunar ta ce sojojin ta ba su da niyar yi wa mulkin damokaradiya karan tsaye

- Kakakin rundunar ya ce dakarun sun kasance, masu biyayya ne ga dokokin Najeriya wadanda suka shimfida mulkin dimokaradiya

Hukumar Sojojin Najeriya ta musanta jita-jitan yunkurin juyin mulkin da wasu ke cewa za’a yi a kasar, inda ta ce sojojin kasar ba su da niyar yi wa mulkin damokaradiya karan tsaye.

A wani taron manema labarai, Kakakin rundunar sojin kasar birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya ce dakarun sun kasance, masu biyayya ne ga dokokin Najeriya wadanda suka shimfida mulkin dimokaradiya.

"Sojoji Najeriya sun ta’allaka ne ga yin biyayya ga shugaban kasa kuma kwamandan sojoji da tsarin mulkin kasa", a cewar Janar Kukasheka.

Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin yunkurin juyin mulki

Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin yunkurin juyin mulki

Rundunar Sojin ta bukaci ‘Yan Najeriya su kwantar da hankalinsu domin babu batun karbar mulki ta hanyar karfi.

KU KARANTA KUMA: Muna bukatar shugabanni masu tsoron Allah a Najeriya – Femi Fani-Kayode

Sai dai Janar Kukasheka ya ce ana gudanar da bincike kan yadda wasu rahotanni suka ce ana zawarcin wasu sojoji domin juyin mulkin. A cewar sa hakki ne na kwamandoji su tsawatar tare da jan kunne.

Wannan na zuwa a yayin da fadar shugaban kasa ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da abin da rundunar sojin kasar ta bayyana kan yunkurin juyin mulkin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis

Saraki, Dogara da mambobin majalisar dokoki na iya barin APC a ranar Alhamis
NAIJ.com
Mailfire view pixel