Uwargidan shugaba Buhari ta fadi me ke bawa mijinta kwarin gwiwa

Uwargidan shugaba Buhari ta fadi me ke bawa mijinta kwarin gwiwa

- Karatowar azumi ta sa kayan abinci hauhawa a farashi, wanda ke gagarar talakka.

- Aisha Buhari ta rabar da kayan abinci a mahaifarta ta Adamawa

- Kwamishinan ilmi na jihar wanda ya wakilci gwamna ya yaba da hobbasar

A jihar Yolar Adamawa, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, na ziyarar aiki inda tayi rabon kayan abinci ga mata da iyalai, ta gaya musu kuma cewa addu'arsu da goyon bayansu da suke bawa maigidan nata shine ummul'aba'isin kwarin gwiwarsa da dagewarsa wajen ganin ya ciyar da rayuwar matan najeriya gaba.

A nasa bangaren kwamishinan ilmi na jihar, Malam Farauta ya nuna farin cikinsa da goyon bayansa ga shirin, inda yace duk wani abu da zai taimakawa mata da talakka, to fa shi yana goyon bayansa.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin yunkurin juyin mulki

Uwargidan shugaba Buhari ta fadi me ke bawa mijinta kwarin gwiwa

Uwargidan shugaba Buhari ta fadi me ke bawa mijinta kwarin gwiwa

Uwar gidan shugaban, ta kara da cewa, "Da bazarku nake rawa, goyon baya da kuka bawa maigida lokacin zabe, shi yasa nima yau na zo nan, domin in nuna muku ban manta da ku ba, ba kuma zan taba mantawa da ku ba."

KU KARANTA KUMA: Muna bukatar shugabanni masu tsoron Allah a Najeriya – Femi Fani-Kayode

Saura dai 'yan kwaqnaki shigaba Buhari ya cika shekaru biyu a karagar mulki, kuma yana kasar ingila a yanzu haka yana karbar magani.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel